Wani dan takarar Sanata a APC ya rasa tikitin jam’iyyar ana gab da zabe

Wani dan takarar Sanata a APC ya rasa tikitin jam’iyyar ana gab da zabe

- Wata babbar kotun tarayya a Enugu ta soke takarar Prince Lawrence Ezeh a matsayin dan takaran kujerar Sanata a yankin gabashin Enugu

- Kotun dai ta maye gurbin Ezeh da Adaku Ogbu Aguocha

Wata babbar kotun tarayya a Enugu ta soke takarar Prince Lawrence Ezeh a matsayin dan takaran kujerar Sanata a yankin gabashin Enugu.

Kotun ta amince da Adaku Ogbu Aguocha, a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na mazabar gabashin Enugu.

Wani dan takarar Sanata a APC ya rasa tikitin jam’iyyar ana gab da zabe

Wani dan takarar Sanata a APC ya rasa tikitin jam’iyyar ana gab da zabe
Source: UGC

A jerin sunayen hukumar zabe, Ezeh ya kasance dan takaran kujerar majalisar dattawa na jam’iyyar APC.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC reshen jihar Neja, ta karbe tikitin takarar kujerar wakilin shiyyar Neja ta Gabas na majalisar dattawa daga hannu Sanata David Umaru ta kuma danka shi a hannun Muhammad Sani Musa.

KU KARANTA KUMA: Kwace akwatin zabe: Buhari ya nuna ainahin halinsa ta hanyar barazana da kisan kai - Atiku

Sauya sunan dan takarar da hukumar INEC ta yi ya biyo bayan hukuncin babbar kotun tarayya, da ta tabbatar da Sani Musa a matsayin wanda ya yi nasarar samun tikitin takara a zaben fidda gwani da aka gudanar yayin da babban zaben kasa ke kan gaba.

Sakamakon hukuncin babbar kotun ya sanya hukumar zabe ta aike da wasika a ranar 15 ga watan Fabrairun 2019 zuwa kwamishinan hukumar reshen jihar Neja, Farfesa Sam Egu, inda ta umarce shi akan sauya sunan Sanata Umaru da na Sani Musa a matsayi marikin tutar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel