Kwace akwatin zabe: Buhari ya nuna ainahin halinsa ta hanyar barazana da kisan kai - Atiku

Kwace akwatin zabe: Buhari ya nuna ainahin halinsa ta hanyar barazana da kisan kai - Atiku

Dan takaran kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoplea Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a jiya Litinin, 18 ga watan Fabrairu yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna “kalan shi tare da rashin girmama kundin tsari mulki”, ta hanyar furta cewa a bakin ran duk wanda yayi yunkurin sace akwatin zabe.

Atiku, a wani jawabin da yayi ta hannun kakinsa, Phrank Shaibu, yace barazana da mutuwa ga mutane a halin shirin gudanar da zabe “kalma ce dake hadda sa rikicin zabe”.

Kwace akwatin zabe: Buhari ya nuna ainahin halinsa ta hanyar barazana da kisan kai - Atiku

Kwace akwatin zabe: Buhari ya nuna ainahin halinsa ta hanyar barazana da kisan kai - Atiku
Source: UGC

Atiku wanda ya nuna rashin amincewarsa akan shirin tura sojoji a zaben 2019, inda yake bayyana hakan a matsayin rashin dacewa ga damokardiyya, yayi Allah wadai da dabarun tsoratarwa da Gwamnatin Tarayya ke shiryawa.

Atiku ya tuna a baya a hira da aka yi da shi a watan jiya a wani shiri mai taken “The Candidates” Atiku ya bada bayani akan kaddamar da hukumar satar zabe, don hukunci akan al’amura da suka shafi laifuffukan zabe kamar yanda yake a dokar kasa.

KU KARANTA KUMA: Dan Abacha ya ba Buhari tabbacin samun kuri’u miliyan 2

A wani lamari na daban, mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar gaggawa da manyan hafsoshi tsaron Najeriya, sifeton yan sanda, Mohammed Adamu, da wasu gwamnonin arewacin Najeriya a ranan Talata, 19 ga watan Febrairu, 2019.

An fara ganawar ne misalin karfe 11 na safe a ofishin shugaban kasa. Manyan hafsoshi tsaron dake hallare sune babban hafsan hukumar tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; babban hafsan sojin sama, Air MArshal Abubakar Sadique, Janar Tukur Buratai; IGP Mohammed Adamu.

Gwamnonin da ke halarce a taron sune gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow; gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima; da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel