A jihar Cross River: Rikicin siyasa ya ja an kashe mutane 3, da yawa sun jikkata

A jihar Cross River: Rikicin siyasa ya ja an kashe mutane 3, da yawa sun jikkata

- Akalla mutane uku aka kashe tare da jikkata wasu da dama a wani sabon hari da 'yan bangar siyasa suka kai garin Bendeghe, jihar Cross River

- Rahotanni sun bayyana cewa wadanda aka kashen mambobin jam'iyyar PDP ne, da suka hada da shugaban jam'iyyar na kundumar a Bendeghe

- Tsawon shekaru kenan ake kallon karamar hukumar Etung a matsayin mahadar tashin fitintinu da suka shafi siyasa a jihar Cross River

Al'ummar garin Bendeghe, karamar hukumar Etung da ke jihar Cross Rivers sun koka kan irin hare haren 'yan bangar siyasa da ake kawai garin nasu.

Rahotanni sun bayyana cewa an kai wani sabon hari a garin a ranar Asabar, makon da ya gabata, inda har mutane ukku suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harbin bindiga.

A yayin da wadanda aka kashen mambobin jam'iyyar PDP ne, da suka hada da shugaban jam'iyyar na kundumar a Bendeghe, wadanda suka tsira da rayukansu, sun alakanta harin ga jam'iyyar APC da ke yankin.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun zargi Obasanjo da ci-da-zuci

A jihar Cross River: Rikicin siyasa ya ja an kashe mutane 3, da yawa sun jikkata

A jihar Cross River: Rikicin siyasa ya ja an kashe mutane 3, da yawa sun jikkata
Source: Twitter

Daya daga cikin wadanda harin ya faru a ganasu ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa 'yan bangar siyasar sun farwa mambobin PDP a yayin da suke sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya na jam'iyyu domin gudanar da zabe lami lafiya.

Al'ummar garin sun yi kira ga jami'an tsaro da kuma hukumomin gwamnati da su kara karfafa sha'anin tsaro a yankin domin dakile tashin hankula musamman a lokacin da zaben ya ke kara matsowa.

Tsawon shekaru kenan ake kallon karamar hukumar Etung a matsayin mahadar tashin fitintinu da suka shafi siyasa a jihar Rivers.

Wani hadimin gwamnan jihar na musamman, Mr Oscar Ofuka wanda ya fito daga yankin ya yi Allah-wadai da wannan hari da aka kai garin.

Ofuka, ya kuma yi kira ga mambobin jam'iyyar PDP da ke a garin da su dau hakuri da kuma kauracewa daukar fansar abun da aka yiwa mambobinsu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel