Da duminsa: EFCC da damke lauyan Atiku kan badakalar $2m

Da duminsa: EFCC da damke lauyan Atiku kan badakalar $2m

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta damke Uyi Giwa Osagie, lauya kuma tsohon ma'ajin tsohon shugaban kasa kuma san takaran kujeran shugaban kasa, Atiku Abubakar.

An damke Osagie ne ranan Litinin bayan damke wani Alhaji Abdullahi Usman, wani shahrarren dan canji dake zaune a Legas, wanda aka kama da jigilar makudan kudi $2m daga filin jirgin saman Abuja zuwa Legas.

Yayinda hukumar EFCC ta kama Usman, wanda mammalakin kamfanin Hasbunallahu BDC LTD ne, ya bayyana cewa lauyan Atiku, Uyi Osagie, ya tura masa kudi $4 miliyan. Ya raba biyu ne yayinda ya kai Legas kuma ya ajiye a bankin Keystone.

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa wannan kudin na Atiku Abubakar wanda zai yi amfani da su wajen zabe. Bayan damkesa, jami'an EFCC sun gudanar da bincike a cikin gidansa dake Ikoyi Reeve inda suka gano takardu dake alakantasa da Atiku.

Ya ki baiwa hukumar goyon baya kuma yana tsare a wajen hukuma.

Kana, wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyanawa Sahara Reporters cewa hukumar INEC ta dage zaben ne domin baiwa Atiku daman samun wasu kudade.

An tuntubi kakakin hukumar, Tony Orilade, amma ya ki magana kan al'amarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel