Rikicin kafin zabe: Yan sanda sun kama mutane 10, makamai da katunan zabe a Akwa Ibom

Rikicin kafin zabe: Yan sanda sun kama mutane 10, makamai da katunan zabe a Akwa Ibom

- Yan sandan jihar Akwa Ibom sun kama mutane 10 da zargin kashe mutum daya da kona motoci 11 kusa da ofishin hukumar INEC a yankin karamar hukumar Obot Akara

- Rundunar ta kuma kama katunan zabe na dindindin akalla guda 179 da katin zabe na wucin gadi guda 27 yayinda ta kama wasu mutane 41 da suka yi ikirarin kasancewa daga cikin masu kiyaye zabe

- Kwamishinan yan sandan jihar yace za a mika wadanda ake zargin ga hukuma don bincike ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa dasu bi doka su kuma shawarci magoya bayansu dasu yi biyayya a lokacin zabe

Rundunar yan sanda reshen jihar Akwa Ibom ta kama mutane 10 da zargin kashe mutum daya da kona motoci 11 kusa da ofishin hukumar INEC a yankin karamar hukumar Obot Akara dake jihar.

Rundunar ta kuma kama katunan zabe na dindindin akalla guda 179 da katin zabe na wucin gadi guda 27 yayinda ta kama wasu mutane 41 da suka yi ikirarin kasancewa daga cikin masu kiyaye zabe amma babu wani shaida a tattare da su da ya tabbatar da hakan.

Yayinda yake magana a taron manema labarai a Uyo, kwamishinan yan sanda, Bashir Makama, wanda ya samu wakilcin kakakin rundunar, DSP Odiko Ogbeche yace ko da yake yan fashin sun cinnawa ofishin hukumar zabe dake a karamar hukumar kudancin Obolo wuta, rundunar sunyi nasara wajen kashe wutan sannan suka ceto kayan hukumar zabe.

Rikicin kafin zabe: Yan sanda sun kama mutane 10, makamai da katunan zabe a Akwa Ibom

Rikicin kafin zabe: Yan sanda sun kama mutane 10, makamai da katunan zabe a Akwa Ibom
Source: UGC

Ya musanta rahoton kafofin labarai cewa rundunar ta kama yan bangan siyasa 400 a jihar, inda ya bayyana cewa mutane 10 kawai aka kama kuma a halin yanzu ba a alakanta su ga kowace jam’iyyar siyasa ba.

KU KARANTA KUMA: Dan Abacha ya ba Buhari tabbacin samun kuri’u miliyan 2

Ya bayyana makamai da aka kwato daga wadanda ake zargi su 10 wanda ya hada da bindigogi 25, kayan ganye da ashana, layu, suman mutum, matattun tsuntsaye, wukake, almakashi, kayan shaye shaye, gatari da wayoyi.

Yace za a mika wadanda ake zargin ga hukuma don bincike ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa dasu bi doka su kuma shawarci magoya bayansu dasu yi biyayya a lokacin zabbuka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel