Amurka ta bayyana yadda APC ta yi nasara a zaben 2015

Amurka ta bayyana yadda APC ta yi nasara a zaben 2015

- Wani Farfesan kasar Amurka, Carl LeVan ya bayyana dalilai da suka tayi tasiri wajen samun nasarar APC da shugaban kasa Buhari a zaben 2015

- A yayin da jam'iyyu da dama suka gudanar da yakin su ne neman zabe kan kudirirrika daban-daban, LeVan ya ce jam'iyyar APC ta gudanar da na ta salon akan tattalin arziki, yaki da rashawa da kuma tabbatar da zabe na gaskiya da adalci

- Farfesan ya ce dimokuradiyya ta taka rawar gani yayin da Najeriya ta sauya salon mulki daga mulkin soji zuwa na farar hula da kawowa yanzu ake ci gaba da cin gajiya

Carl LeVan, Farfesan nazari akan harkokin kasa da kasa na Jami'ar Amurka da ke birnin Washington DC, ya fayyace sakamakon binciken sa da ya gudanar dangane da dalilai da suka yi tasiri wajen samun nasara jam'iyyar APC a zaben 2015.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, Farfesa LeVan ya bayyana dalilan sa yayin fashin baki gami da sharhin sabon littafin sa da wallafa kan siyasar Najeriya a jiya Litinin cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Amurka ta bayyana yadda APC ta yi nasara a zaben 2015

Amurka ta bayyana yadda APC ta yi nasara a zaben 2015
Source: Depositphotos

Farfesa LeVan ya zayyana cewa, a yayin da jam'iyyu da dama suka gudanar da yakokin su na neman zaben kan akidu daban-daban a 2015, jam'iyyar APC ta gudanar da na ta salon yakin zabe kan kudirin habaka tattalin arziki, yaki da rashawa da kuma tabbatar da zabe mai aminci.

Da ya ke tabbatar da madogarar wannan bincike, LeVan ya ce wannan muhimman ababe uku da ya wassafa sun taka rawar gani tare da tasirin gaske wajen samun nasarar jam'iyyar APC a zaben 2015.

KARANTA KUMA: Rikicin magoya bayan APC da PDP ya nemi hallaka Yarinya 'yar shekara 11 a jihar Osun

Ya ci gaba da cewa, sakamakon hankoron habaka tattalin arzkin kasar nan musamman ta fuskar yakar cin hanci da rashawa, akidar addini ko kuma kabilanci ba ta yi tasiri ba a zukatan masu kada kuri'a yayin zaben 2015.

LeVan ya kara da cewa, dimokuradiyya ta taka rawar gani tun yayin da Najeriya ta sauya salo na tsarin shugabanci daga mulkin soji zuwa na farar hula da kawowa yanzu ake ci gaba da cin gajiya a kasar nan.

Tarihi ya tabbatar da cewar, jam'iyyar APC ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi nasara yayin zaben 2015 inda ta ci galaba kan tsohon shugaban kasa mai ci a karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, Goodluck Ebele Jonathan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel