Rikicin magoya bayan APC da PDP ya nemi hallaka Yarinya 'yar shekara 11 a jihar Osun

Rikicin magoya bayan APC da PDP ya nemi hallaka Yarinya 'yar shekara 11 a jihar Osun

Mun samu cewa arangama ta rikici da tsananin adawa tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da PDP, ta yi sanadiyar asarar dukiya yayin da kuma azal ta afkawa wata yarinya 'yar shekara 11 a jihar Osun da ke Kudancin Najeriya.

Da sanadin kafar watsa labarai ta Sahara Reporters mun samu cewa, tsawon kwanaki uku kenan kawowa yanzu al'ummar yankunan Iwara, Olowu, Atorin da kuma Lapide na jihar Osun na ci gaba da zaman dar-dar a sakamakon mummunan rikici tsakanin magoya bayan manyan jam'iyyu biyu na kasar nan na PDP da APC.

Rikicin magoya bayan APC da PDP ya nemi hallaka Yarinya 'yar shekara 11 a jihar Osun

Rikicin magoya bayan APC da PDP ya nemi hallaka Yarinya 'yar shekara 11 a jihar Osun
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan mummunan rikici ya yi sanadiyar asarar dukiya mai tarin yawa yayin da kuma azal ta harbi na harasashin bindiga ya afkawa wata yarinya mai shekaru 11 kacal a doron kasa.

Hukumar 'yan sandan jihar Osun yayin tabbatar da aukuwar wannan mugun ji da mugun gani, ta bayyana cewa a halin yanzu Yarinyar na ci gaba da samun kyakkawar kulawa a asibitin koyarwa na Obafemi Awolowo inda ta ke zaman jinya.

KARANTA KUMA: Tuna baya: Yadda hukumar INEC ta dage zaben 2011

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Abiodun Ige a jiya Litinin ya bayyana cewa, hukumar sa za ta gudanar da binciken diddigi domin gano ba'asi na aukuwar tarzomar tare da gargadin 'yan siyasa da su kauracewa haddasa ta'ada a tsakankanin al'ummar jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel