Ku daina alakanta ayyukanmu da Lawal Daura - SSS ta gargadi 'yan Nigeria

Ku daina alakanta ayyukanmu da Lawal Daura - SSS ta gargadi 'yan Nigeria

- SSS ta gargadi 'yan Nigeria da su kauracewa alakanta ayyukanta da tsohon shugaban hukumar, Lawal Daura

- Akwai radi-radin da ke yawo na cewar har yanzu Mr Daura na da ikon fada a ji a hukumar ta SSS, kuma yana da matsugunni a rukunun gidajen ma'aikatan hukumar

- A ranar 7 ga watan Agusta, 2017, mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbaji ya kori Daura daga mukamin, biyo bayan mamaye majalisar tarayya da nufin juyin mulki

Hukumar tsaro ta SSS ta gargadi 'yan Nigeria da su kauracewa alakanta ayyukanta da tsohon shugaban hukumar, Lawal Daura. Hukumar tsaron ta fararen kaya ta ce mutane su daina cewa Mr Daura na da ikon fada a ji a harkokin hukumar, watanni kadan bayan korarsa daga shugabancinta.

A shekarar 2015, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mr Daura a matsayin babban daraktan hukumar tsaron ta DSS, sannan a ranar 7 ga watan Agusta, 2017, mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbaji ya kori Daura daga mukamin, biyo bayan badakalar da ta afku sakamakon mamaye majalisar tarayya da nufin gudanar da juyin mulki.

KARANTA WANNAN: Kowa ya debo da zafi: APC na caccakar Atiku kan alkawarin kare barayin gwamnati

Ku daina alakanta ayyukanmu da Lawal Daura - SSS ta gargadi 'yan Nigeria

Ku daina alakanta ayyukanmu da Lawal Daura - SSS ta gargadi 'yan Nigeria
Source: UGC

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa a baya rundunar 'yan sanda ta cafke Mr Daura inda har ta tsare shi na wani lokaci, daga bisani ta sallame shi ba tare da bayyana dalilin hakan ba.

Akwai radi-radin da ke yawo na cewar har yanzu Mr Daura na da ikon fada a ji a hukumar ta SSS, kuma yana da matsugunni a rukunun gidajen ma'aikatan hukumar.

Sai dai a ranar Talata, a cikin wata sanarwa, hukumar ta SSS ta ce tana sane da wannan labarin kanzon kuregen da ake yadawa, inda ta gargadi jama'a da su kauracewa alakanta ayyukanta da tsohon darakta janar na hukumar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel