Atiku zai kayar da Buhari da tazara mafi girma – Kungiyar kamfen tayi ikirari

Atiku zai kayar da Buhari da tazara mafi girma – Kungiyar kamfen tayi ikirari

- Kungiyar kamfen din Jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Sanata Ighoyota Amori, ya baAtiku Aubakar tabbacin samun nasara a zaben da za a gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu

- Amori ya koka akan dage zaben ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu da hukumar zabe mai zaman kanta tayi

- Sanatan yayi zargin cewa APC ta dauki hanyar magudin zabe a kasar, inda yayi misali da zabukan gwamna da aka yi kwanaki a jihohin Ekiti da Osun

Kungiyar kamfen din Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) karkashin jagorancin Sanata Ighoyota Amori, ya ba dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Aubakar tabbacin samun nasara a zaben da za a gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Amori ya koka akan dage zaben ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu da hukumar zabe mai zaman kanta tayi inda ya bayyana hukuncin hukumar a matsayin tsananin gazawa, da kuma biyayya ga gwamnatin APC.

Atiku zai kayar da Buhari da tazara mafi girma – Kungiyar kamfen tayi ikirari

Atiku zai kayar da Buhari da tazara mafi girma – Kungiyar kamfen tayi ikirari
Source: Depositphotos

Ya kara da cewa INEC ta gaza cika tsamannin yan Najeriya da dama, sanatan yayi zargin cewa APC ta dauki hanyar magudin zabe a kasar, inda yayi misali da zabukan gwamna da aka yi kwanaki a jihohin Ekiti da Osun, inda a cewarsa an samu matsalar siyan kuri’u da yawa.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta yi martani kan furucin da maigidanta yayi game da masu sace akwatin zabe

Amori ya ci gaba da zargin cewa idan har hukumar zabe ta ci gaba da shirinta naa magudi a zabe mai zuwa don taimakawa jam’iyya mai nmulki, toh za su fuskanci turjiya mai karfi daga yan Najeriya da kasashen duniya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel