Hukumar Soji ta tsawatar wa masu kokarin tada zaune tsaye a kudancin Najeriya lokacin zabuka

Hukumar Soji ta tsawatar wa masu kokarin tada zaune tsaye a kudancin Najeriya lokacin zabuka

- Hukumar sojin Najeriya ta ja kunnen yan bangar siyasa akan tada hargitsi yayin zabe

- Hukumar tace bayanin sirri hedkwatar ta samu akan wasu yan siyasa sun samar da makamai ga yan bangar siyasa

- Sojin sun ja kunnen ne sakamakon umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan halaka barayin akwatin zabe a take

Hukumar Soji ta tsawatar wa masu kokarin tada zaune tsaye a kudancin Najeriya lokacin zabuka

Hukumar Soji ta tsawatar wa masu kokarin tada zaune tsaye a kudancin Najeriya lokacin zabuka
Source: Depositphotos

Hukumar sojin Najeriya ta ja kunnen cewa zata dau tsauraran matakai akan yan bangar siyasa da ka iya kawo hargitsi a zaben ranar asabar a Niger Delta.

A takardar da mataimakin jami'in hulda da jama'a na sojin, Colonel Aminu Iliyasu, yace jan kunnen ya biyo bayan bayanin da aka mika ga hedkwatar kashi na 6 na sojin Najeriya, akan shirin ta'addanci a yankin Niger Delta.

Iliyasu yace, "Bayanin sirri da hedkwatar ta samu shine mugun shirin da wasu yan siyasa na yankin samar makamai da kuma daukar nauyin yan ta'adda da kuma amfani da kayan sojin don yaudarar mutane a guraren jefa kuri'a don biyan bukatun su na siyasa."

Kamar yanda ya fada, "Ana samo tushen da aka samo makaman da kuma wadanda aka hada baki dasu suka kai musu."

Mai magana da yawun sojin ya kara da cewa duk wanda aka kama da laifin hargitsa zabe zai fuskanci fushin hukuma.

GA WANNAN: Shugaban ASUU da aka dakatar ya fara manyan tone-tone

A yayin da yake tabbatarwa da jama'an Niger Delta isasshen tsaro yayin da kuma bayan zabe, Babban kwamandan kashi na 6 na sojin Najeriya, Manjo janar, Jamil Sarham, yayi godiya ga mutane akan abinda ya kwatanta da hadin kai da taimako ga sojin, ballantana ta bangaren yada bayanai.

Jan kunnen daga sojin ya biyo bayan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari ga jami'an tsaro akan su hukunta barayin akwatin zabe yayin zabe mai zuwa.

Umarnin da shugaban kasa ya bada a ranar litinin ya jawo cece ku ce a wajen yan Najeriya ballantana yan jam'iyyar adawa ta PDP wanda suke ta sukar ra'ayin ba kakkautawa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel