Sakataren PDP na jihar Uzor Kalu ya ajje aikinsa ana tsaka da tsare-tsaren cin zabe

Sakataren PDP na jihar Uzor Kalu ya ajje aikinsa ana tsaka da tsare-tsaren cin zabe

- Wani jagora a jam'iyar PDP ya ajjiye mukamin sa a matsayin sa na sakataren tsare-tsaren jam'iyar

- Ya ajjiye mukamin nasa ne sanaddiyar ciyaman din jam'iyar ta PDP

- Yace an janyeshi daga duk wani abu daya shafi jam'iyar tun a shekara ta 2016

Sakataren PDP na jihar Uzor Kalu ya ajje aikinsa ana tsaka da tsare-tsaren cin zabe

Sakataren PDP na jihar Uzor Kalu ya ajje aikinsa ana tsaka da tsare-tsaren cin zabe
Source: Depositphotos

A ranar Talata ne daya daga cikin jagororin jam'iyar PDP St. Moses Ogbonna ya bayyana cewa ya ajjiye mukamin sa a jam'iyar.

Ogbonna ya bayyana alakar sa da gwamna Okezie Ikpeazu da kuma ciyaman na jam'iyar Sir Johnson Onuigbo wanda shine musabbabin ajjiye mukamin nasa.

Ya rubuta takaddar barinshi aikin ne inda ya bayyana cewa an cireshi daga duk wasu al'amura da suka shafi jam'iyar tun a shekara ta 2016.

GA WANNAN: PDP da APC ne suka janyo dage zaben nan, dan takarar shugaban kasa Moghalu yayi zargi

Ya kara da cewa ana neman rayuwar sa saboda wani bayani daya fitar na cewa anayin abinda bai kamata ta ba da kuma kafa sabbin dokoki a jam'iyar.

Ogbonna yana daga cikin 'yayan jam'iyar guda Goma sha Tara (19) wadanda aka bayyana cewa a 27 watan Nuwamba shekara ta 2018 sunki aminta da nadin ciyaman na jam'iyar.

Anyi kokarin jin ta bakin shi ciyaman din jam'iyar ta PDP a jihar Abia saidai abin ya faskara saboda matsalar na'ura.

Wani na kusa da ciyaman din ya bayyana cewa baya gari yana Abuja dan gudanar da wani taro wanda zai guda a ranar Talata.

Ana kan-kan-kan a wasu jihohi da jigoginta suke sauya jam'iyya ko dai ga babbar jam'iyya mai adawa ko zuwa mai mulki, dab da zaben makonnan.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel