Hukumar Kwastam na kan bincike kan harbi da bindiga, bayan sun halbe wani murus

Hukumar Kwastam na kan bincike kan harbi da bindiga, bayan sun halbe wani murus

- Hukumar Customs ta fara tuhumar ma'aikatan ta bisa sakaci wanda ya janyo rasa rai

- Duk da cewa a farko hukumar taki aminta da hakan inda tace hakan ya faru ne bada ganganci ba

- Idan har an samu ma'aikatan da laifi babu shakka za'a hukuntasu kamar yanda ya kamata

Hukumar Kwastam na kan bincike kan harbi da bindiga, bayan sun halbe wani murus

Hukumar Kwastam na kan bincike kan harbi da bindiga, bayan sun halbe wani murus
Source: UGC

Hukumar Customs din Najeriya (NCS) tace ta fara tuhumar ma'aikatan ta hanyar tambayoyi bisa ga abinda ya faru a ranar Lahadi a Ijebu Ode road.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar Mr Joseph Attah ne ya bayyana haka a yayin da yake wata tattaunawa da NAN a ranar litinin a Abuja.

Ana ta yada wani bidiyo a kafafen sadarwa wanda ke nuni da wani jami'in hukumar ta customs ya harbi wani fasinja dake cikin wata motar kasuwa wanda take ya mutu, duk da cewa NCS bata aminta da hakan ba tace ba bisa ganganci akayi hakan ba.

Attah yayi bayani cewa mataimakin shugaban hukumar Zone A Ekekezie Kessy ya ziyarci reshensu dake Ikeja a ranar Litinin dan yiwa jami'an dake gurin tambayoyi.

GA WANNAN: An zargi Obasanjo da INEC da hada kai don taimakawa PDP da dage zabe

Yace za'a gudanar da binciken ne dan a gano musabbabin afkuwar wannan abu wanda har ya janyo hasarar rai.

"Ana gudanar da bincike ta hanyar tambayoyi bisa ma'aikatan da abin ya shafa da kuma yanda suke rike makaman su".

"Idan har an samesu da laifi to babu shakka za'a hukuntasu daidai da laifin da suka aikata".

Ya kara da cewa babu dadi ace an rasa rai a lokacin da kake gudanar da aiki.

Daga karshe yayi kira ga al'umma da su kula wajen kallar abinda da aka wata a kafafan sadarwa saboda wasu daga cikin ire iren abubuwan ka iya canyo canjawar tunani.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel