Gwamna Ifeanyi Okowa ya ziyarci Iyalin Hadimin sa da aka kashe

Gwamna Ifeanyi Okowa ya ziyarci Iyalin Hadimin sa da aka kashe

- Gwamna Ifeanyi Okowa ya ziyarci Iyalin Hadimin sa da aka kashe kwanan nan

- Jiya Okowa ya taka kafa-ya-kafa zuwa wajen Ngozi Ijei da aka hallaka Mijin ta

Gwamna Ifeanyi Okowa ya ziyarci Iyalin Hadimin sa da aka kashe

Gwamna Okowa da Mai dakin da wani Hadimin sa ya mutu ya bari
Source: Twitter

Mun samu labari cewa gwamnan jihar Delta Mista Ifeanyi Okowa ya ziyarci Iyalin wani hadimin sa da aka kashe yayin da ake shirin zaben shugaban kasa kwanan nan. Daga baya dai an dakatar da zaben zuwa karshen makon nan.

Ifeanyi Okowa ya taka da kafar sa ya leka gidan Madam Veronica Ijei wanda ta rasa Mijin ta a hannun wasu ‘yan bindiga a Garin Ekpan da ke cikin karamar Uvwie a jihar Delta. Iyalin gwamnan sun nuna takaicin rashin da aka yi.

KU KARANTA: An yi rashin wani babban ‘dan siyasa a Jihar Yobe jiya

Gwamnan yake cewa yayi kokarin ganin an samu kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin na Ekpan a cikin shekarun da yayi yana mulki, kafin ‘yan bindiga su kashe Hadimin sa Lawrence Ngozi Akpomiemie a makon jiya

Mista Okowa yayi wannan bayani ne lokacin da ya ziyarci Mai dakin da Mista Lawrence Ngozi Akpomiemie ya bari. Gwamnan yake cewa kisan da aka yi wa babban Hadimin na sa yana da nasaba da halin siyasar da ake ciki a yanzu.

Gwamna Okowa yace Marigayin yayi wa jihar sa kokari a lokacin yake rike da ofishin mai bada shawara a gwamnati. Har wa yau dai gwamnan yayi addu’a ga Iyalin mamacin su samu karfin jure rashin sa tare da nema masa kyakkyawan karshe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel