Neman shugaban INEC ya yi murabus: MInista ya yi kaca-kaca da Oshiomhole

Neman shugaban INEC ya yi murabus: MInista ya yi kaca-kaca da Oshiomhole

- Ministan sadarwa Adebayo Shittu ya yi kaca-kaca da shugaban APC, Adams Oshiomhole a kan neman shugaban INEC, Mahmood Yakubu ya yi murabus

- Adebayo Shittu ya ce babu wanda ya bukaci Oshiomhole ya yi murabus duk da cewa an samu tangarda sosai a zabukkan cikin na jam'iyyar APC

- Ministan ya ce dukkan dan adam yan iya kuskure kuma canja shugaban INEC a halin yanzu zai mayar da shirin zaben baya

Ministan sadarwa Alhaji Adebayo Shittu ya soki shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole a kan neman shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC, Yakubu Mahmood ya yi murabusa daga kujerarsa saboda dage zabe da ya yi.

A yayin da ya ke magana da manema labarai a ranar Litinin, Shittu ya ce tsohon gwamnan na jihar Edo bashi da hurumin ya nemi wani ya yi murabus duba da cewa shine ya gudanar da zabukkan cikin gida mafi muni a shekarun baya-bayan nan.

DUBA WANNAN: Adam Zango ya yi karin haske a kan kai masa farmaki saboda zagin Buhari

Neman shugaban INEC ya yi murabus: MInista ya yi kaca-kaca da Oshiomhole

Neman shugaban INEC ya yi murabus: MInista ya yi kaca-kaca da Oshiomhole
Source: UGC

Ya ce idan Yakubu ya dauki shawarar Oshiomhole ya yi murabus, hakan zai shafi zaben da aka daga.

Ya ce, "A lokacin da Oshiomhole ya gudanar da zabukkan cikin gida mai muni, wane ya bukaci ya yi murabus?"

A cewarsa, idan shugaban INEC na yanzu ya yi murabus, dole za a sake dage zaben saboda sabon shugaban INEC ya samu damar shirya sabon zabe.

"Bana goyon bayan shugaban INEC ya yi murabus. Dukkan dan adam yana kuskure. Dage zaben da INEC tayi ba shi da wata nasaba da wani jam'iyyar siyasa. Idan Oshiomole ya bukaci shugaban INEC ya yi murabus, shima ya kamata ya fara shirin murabus daga kujerarsa a matsayin shugaban jam'iyyar mu," a cewar Shittu.

Al'umma da dama suna ta bayyana ra'ayoyinsu a kan dage zaben da hukumar INEC, wasu na goyon bayan INEC yayin da wasu ke ganin babu wani dalilin da zai sanya a dage zaben duba da cewa hukumar ta kwashe shekaru hudu suna shirin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel