Aisha Buhari ta yi martani kan furucin da maigidanta yayi game da masu sace akwatin zabe

Aisha Buhari ta yi martani kan furucin da maigidanta yayi game da masu sace akwatin zabe

Uwargidan Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari a jiya, Litinin, 18 ga watan Fabrairu ta yaba ma furucin mai gidanta a wani rubutu da tayi a shafin twitter yayinda take goyon ayan jawabin da yayi akan masu magudin zabe.

A wajen taron shugabannin APC da ya gudana a Abuja shugaan kasa Muhammadu Buhari yayi gargadi da kakkausar murya akan wadanda ke yunkurin hargitsa zaben da aka dag eta hanyar sace akwatin zabe.

“Ina ba sojoji da yan sanda umurni kan kada su ji tausayi kowa,” inji Buhari.

“Duk wanda yake ganin yana da kafa da zai iya jagorantar tawagar yan iska don kwace akwatunan zabe ko hargitsa tsarin zabe , a bakin ransa," cewar Shugaban kasar.

Aisha Buhari ta yi martani kan furucin da maigidanta yayi game da masu sace akwatin zabe

Aisha Buhari ta yi martani kan furucin da maigidanta yayi game da masu sace akwatin zabe
Source: Getty Images

Ko da yake furucin shugaban kasar ya hadu da cikas inda mutane da dama suka soki lamarin. Sai dai uwargidan shugaban kasar ta nuna goyon baya ga gargadin da maigidan nata yayi da kuma umurnin da ya ba hukumomin tsaro akan masu tayar da tarzoma a lokacin zabe.

A rubutu da ta wallafa a shafinta na twittte a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu ta bayyana cewa Buhari na hanyar kai Najeriya mataki na gaba.

KU KARANTA KUMA: Dage zabe ya sa dala ta karye warwas a Najeriya

Mutane da dama sun je shafukansu na zumunta ciki harda twitter don yin sharhi, cewa alamu sun nuna cewa Shugaban kasar zai dawo a matsayin “Janar”a zagayensa na biyu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel