Babban jami’in hukumar INEC da ya yi sanadiyyar zage zabe zai gurfana gaban DSS

Babban jami’in hukumar INEC da ya yi sanadiyyar zage zabe zai gurfana gaban DSS

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS, ta gayyaci wani babban jami’i a hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, wanda ya sabbaba dage zaben 2019 da kwanaki bakwai, Mista Okechukwu Ibeanu, domin amsa tambayoyi bisa wasu tuhume tuhumen da take masa.

Mista Ibeanu, shine kwamishinan INEC mai kula da tsare tsare da zirga zirga, sa’annan shine ke wakiltar yankin kudu maso gabashin Najeriya a hukumar, sai dai ana tuhumarsa da sakaci wajen gudanar da aikinsa, wanda hakan yasa dole aka dage zaben 2019.

KU KARANTA: Da dumi dumi: EFCC ta kama babban mai daukan nauyin takarar Atiku Abubakar

Babban jami’in hukumar INEC da ya yi sanadiyyar zage zabe zai gurfana gaban DSS

Ibeanu
Source: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an jiyo shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu yana bayyana bacin ransa game da dage zaben na 2019, wanda ya danganta hakan ga bita da kullin da wasu keyi ma hukumar, da kuma rashin isan kayan aiki zuwa inda suka kamata cikin lokaci.

A matsayinsa na kwamishinan tsare tsare da zirga zirga, hakkin tabbatar da isan kayan aikin zabe zuwa inda suka kamata ya rataya ne a wuyan Ibeanu, bayan an amshe mukamin daga hannun Amina Zakari a watan Oktoban shekarar data gabata.

Ana sa ran da misalin karfe 2 na ranar Talata ne Ibeanu zai gurfana gaban hukumar DSS a babban ofishinta dake babban birnin tarayya Abuja, sai dai an jiyo Ibeanu yana bayyana ma abokansa cewa ana masa barazana.

Rahotanni sun tabbatar da cewar anyi kutse cikin gidansa dake garin Enugu, haka zalika an fasa motarsa, inda aka kwashe masa kayayyaki da dama daga ciki har da kwamfutar tafi da gidanka. Sai dai dama an jiyo shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin gudanar da binciken INEC bayan zabe don gano gaskiyar abinda yasa ta dage zaben.

Amma a wani yanayi na waiwaye adon tafiya, an bankado wata kasida da Farfesa Ibrahim Jibrin ya rubuta a shekarar 2015 lokacin da aka nada Ibeanu mukamin kwamishinan INEC, inda ya zargeshi da niyyar dabbaka manufofi da muradin kungiyoyin rajin kafa kasar Biyafara a INEC.

A yanzu dai ana nan ana tafka muhawara akan wannan tsohuwar kasida ta Farfesa Ibrahim, inda wasu ke danganta tsaikon da aka samu a zaben 2019 ga burin Ibeanu na tabbatar da manufofin yan Biyafara, wanda hakan har sun fara kiraye kirayen a tsigeshi da taken #INECIbeanuMustGo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel