Sai Shugaba Buhari ya tashi da kuri’a akalla miliyan 3 a Jihar sa – Gwamna Masari

Sai Shugaba Buhari ya tashi da kuri’a akalla miliyan 3 a Jihar sa – Gwamna Masari

- Aminu Masari yace dage zabe ba zai kawowa Buhari cikas a Katsina ba

- Gwamna Masari yace Shugaban kasar zai samu kuri’u miliyan 3 a zabe

- Masari yace dakatar da zaban da INEC tayi sam bai fa ba sa mamaki ba

Sai Shugaba Buhari ya tashi da kuri’a akalla miliyan 3 a Jihar sa – Gwamna Masari

Masari yace s je a dawo sai Buhari ya tashi da miliyoyin kuri’u a Katsina
Source: UGC

Mun ji cewa Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa dakatar da zabe da aka yi bayan an shirya a makon da ya gabata, ba zai hana Muhammadu Buhari samun nasara a jihar ba a karshen makon nan.

Aminu Masari ya bayyanawa manema labarai jiya cewa matakin da hukumar INEC ta dauka na dakatar da zaben shugaban kasa ba zai canza ra’ayin jama’a ba. Gwamna Masari yace duk da haka jama’a za su sake zaben Buhari.

KU KARANTA: An gano shirin da PDP ta kitsawa a Jihohi 36 a zaben 2019

Mai girma Aminu Bello Masari yake cewa taron jama’ar da aka gani a jihar Katsina a Ranar Alhamis lokacin da shugaba Buhari ya dawo gida domin zabe, ya nuna cewa APC za ta samu akalla kuri’a miliyan 3 a zaben.

Gwamnan yace Katsinawa sun shirya marawa Buhari baya ya zace wani karo a zaben na 2019. Haka zalika gwamnan na jam’iyyar APC yace dakatar da zaben da aka yi bai zo masa da mamaki ba domin ya san halin INEC.

Alhaji Aminu Masari ya kuma dauke laifin dakatar da zaben daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yace laifin hukumar INEC mai zaman kan-ta za a gani bayan ta sanar da cewa ta shiryawa zaben tsaf.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel