Da dumi dumi: EFCC ta kama babban mai daukan nauyin takarar Atiku Abubakar

Da dumi dumi: EFCC ta kama babban mai daukan nauyin takarar Atiku Abubakar

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta cafke wani babban mai kula da kudaden da ake kashewa a takarar dan takarar shugaban kasa na jam’yyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, mai suna Uyi Giwa-Osagie.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata majiya ta karkashin kasa ta bayyana cewa EFCC ta kama Uyi ne a ranar Litinin, 18 ga watan Feburairu, amma ta sakeshi bayan ta gudanar da bincike akansa tare da yi masa wasu yan tambayoyi na tsaown sa’o’i 9 a ofishinta.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun gamu da ruwan azaba daga wajen Sojojin Najeriya

Da dumi dumi: EFCC ta kama babban mai daukan nauyin takarar Atiku Abubakar

Uyi yana waya tare da Atiku Abubakar
Source: UGC

Shi dai Uyi babban lauya ne, kuma shine babban mai kula da duk kudin da ake kashewa a takarar Atiku Abubakar, wanda ya hada har da yakin neman zabe, don haka yana daya daga cikin amintattu, na hannun dama kuma na kusa da Atiku.

“Atiku baya kashe kudi a takararsa kai tsaye, Uyi Giwa ne ke kashe duk kudin da ake bukata a yakin neman zaben Atiku, ta hannunsa Atiku yake antaya kudi cikin yakin neman zabensa.

“Don haka kamashi da EFCC tayi ka iya haifar da takarar Atiku, musamman game da zirga zirgan wakilan zabe da zasu kare mana kuri’unmu a kowanne rumfa da kuma biyansu kudadensu.” Inji wani kusa a kwamitin yakin neman zaben Atiku.

Shima tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonatha, Reno Omokri, wanda a yanzu yana cikin jiga jigan dake tsara yakin neman zaben Atiku Abubakar ya bayyana bacin ransa da kamen da EFCC ta yi ma Uyi, inda yace anyi haka ne don yi ma takarar Atiku zagon kasa.

“Akan me EFCC za ta kama lauyan Atiku Uyi tafe da jami’an Yansanda guda 25 dauke da muggan makamai? Kodai dama shirin su kama duk wanda ke tare da Atiku yasa suka dage zaben? Laifi ne ka zama lauyan Atiku? Ya zama dole EFCC ta bayyana ma yan Najeriya dalilin kama Uyi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel