Mayakan Boko Haram sun gamu da ruwan azaba daga wajen Sojojin Najeriya

Mayakan Boko Haram sun gamu da ruwan azaba daga wajen Sojojin Najeriya

Dakarun rundunar Sojan Najeriya ta yi ma mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram kisan kiyashi a wani dauki ba dadi da suka yi da juna a ranar Asabar, 16 ga watan Feburairu a garin Gajigana na jahar Borno, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mataimakin kaakakin runduna ta 7 na Sojan kasa, Kanal Ado Isa ne ya sanar da haka, inda yace wannan karon batta ya wakana ne yayin da yan ta’addan suka yi kokarin kutsa kai cikin rundunar Sojin dake jibge a Gajigana, inda suka tarar da abinda yafi karfinsu.

KU KARANTA: Rundunar Sojan Najeriya ta dauki alwashin cika umarnin Buhari akan barayin akwatin zabe

Kaakakin yace Sojoji sun samu tabbacin karkashe mayakan na Boko Haram da dama ne a washegari yayin da suke bin sawun yan ta’addan, inda suka tarar da jini ya yi malale a ko ina akan hanyar da yan ta’addan suka bi suka tsere, wanda hakan ya nuna sun kwashe gawarwakin wadanda aka kashe kenan.

Daga cikin makaman da Sojoji suka kwato sun hada da gurneti guda daya, alburusai daban daban da kuma na’urar hangen nesa da daddare. Shima babban kwamandan runduna ta bakwai, Abdulmalik Bulama Biu ya kai ziyarar gani da ido zuwa wajen da aka yi arangamar.

A jawabinsa, Birgediya Janar Bulama ya bayyana jin dadinsa game da jarumtar da Sojojin suka nuna, sa’annan ya jinjina musu bisa jajircewar da suka dade suna nunawa a yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas, don haka yayi kira a garesu dasu cigaba da zage damtse.

Daga karshe hukumar Soji ta baiwa dakarun sabbin makamai, da karin alburusai da dama, kamar yadda babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Tukur Yusuf Buratai ya umarta, inda yace yana fatan haka zai kara musu kwarin gwiwar cigaba da gudanar da aikinsu.

A wani labarin kuma, wani kazamin karon battar dakarun Sojin Najeriya da mayakan Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar yan ta’adda guda biyar, yayin da Sojoji suka yi asarar jami’ai guda hudu, daga cikinsu har da wani hafsan Soja.

Mukaddashin kaakakin rundunar, Kanal Sagir Musa ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa daya fiyar a ranar Lahadi, 17 ga watan Feburairu, inda yace sun kashe yan ta’addan biyar a lokacin da suka yi kokarin tarwasa sansanin Sojojin da misalin karfe 6:5 na yammacin Asabar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel