2019: Jam’iyyar PDP ta ware Dala Miliyan 3 domin sayen kuri’a

2019: Jam’iyyar PDP ta ware Dala Miliyan 3 domin sayen kuri’a

- Jami’an tsaro sun samu rahoton cewa PDP na shirin sayen kuri’ar jama’a a zaben bana na 2019

- Rahotannin da ake samu ya nuna cewa an ware Miliyan $3 domin wannan danyen aiki a kasar

- Akwai hannun wani tsohon Ma’aikacin INEC da wasu manya a kasar da hannu dumu-dumu

2019: Jam’iyyar PDP ta ware Dala Miliyan 3 domin sayen kuri’a

Ana kishin-kishin PDP za ta kashe Dala Miliyan 3 a kowace Jiha
Source: Twitter

Mun ji labari akwai kishin-kishin da ake yi na cewa jam’iyyar hamayya ta PDP ta ware wasu makudan kudi domin sayen kuri’ar Talakawa a zaben da za ayi a Najeriya. Har dai ta kai canza Dala zuwa Naira yana nema ya gagara.

Kamar yadda mu ka ji, wani rahoto da jami’an tsaron kasar su ke samu, ya nuna cewa jam’iyyar PDP ta ware kudi har Dala Miliyan 3 watau sama da Naira Biliyan 1.8 a kowace jiha a Najeriya domin a saye kuri’a a lokacin zabe.

KU KARANTA: Gwamnan PDP na hada kai da Shugaban INEC a zaben 2019

Jam’iyyar hamayyar ta raba wannan kudi ne zuwa kowace jihar kasar, sai dai hukumomin EFCC da kuma DSS sun sa wa masu harkar canjin Dala ido, don haka yanzu yake wahalar manyan jam’iyyar adawar su iya canza kudin.

Wannan bincike na musamman da jami’an tsaro su ke yi ya bayyana cewa PDP ta fake ne da sunan zirga zirgar zabe inda ta warewa kowace jihar abin da ya kusa kai Naira biliyan 2 domin ta ci zaben bana ta hanyar rabawa masu zabe kudi.

KU KARANTA: 2019: Atiku Abubakar ya maka Gwamnatin Buhari a gaban Kotu

Babban jam’iyyar adawar za ta kashe Dala miliyan 111 (Fiye da Naira biliyan 60) a jihohi 36 na kasar kenan a zaben da za ayi a karshen makon nan wajen sayen kuri’a. Ana da rumfunan zabe sama da 120, 000 yanzu haka a Najeriya.

Daga cikin wadanda ake tunani su ke da hannu a wannan aiki inji jaridar The Nation akwai wani tsohon babban jami’in INEC da kuma wani babba daga cikin kwamitin nan da aka kafa domin kawo zaman lafiya a zaben Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel