Bahallatsar $1,000,000: Kwamishinan INEC ya musanta karbar cin hanci daga wajen Atiku

Bahallatsar $1,000,000: Kwamishinan INEC ya musanta karbar cin hanci daga wajen Atiku

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, reshen jahar Adamawa, Malam Kashim Gaidam ya musanta wani rahoto da jama’a ke yayatawa na cewa wai ya amshi dala miliyan daya a matsayin kudin goro daga dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin ne aka samu wani rahoto dake nuna cewa wai Gaidam yayi watsi da tayin cin hancin dala miliyan daya da Atiku Abubakar ya yi masa domin ya tayashi murde zabe a jahar Adamawa.

KU KARANTA; Gwamnatin Kaduna da Bankin duniya zasu gina babban kamfanin sarrafa citta

Bahallatsar $1,000,000: Kwamishinan INEC ya musanta karbar cin hanci daga wajen Atiku

Atiku
Source: UGC

Baya ga kudin da rahoton ta bayyana cewa Atiku yayi ma Gaidamn tayi, wai kuma har da kyautan katafaren gidan alfarma a kasar Dubai zai samu idan har ya yarda, sai dai Gaidam ya musanta rahoton gaba daya.

A cikin martanin da Gaidamn ya yi da yammacin Litinin, 18 ga watan Feburairu yace bai taba ganin Atiku ido da ido ba, don haka ta yaya zai yi masa wannan gwaggaban tayi idan har bai sanshi ba? Don haka yayi alkawarin daukan matakin shigar da kara a gaban kotu bisa kokarin bata masa suna da aka yi.

“Ban taba ganin Atiku ba a rayuwata, kuma ina da tabbacin Atiku kansa bai san kamannina ba saboda bamu taba haduwa gaba da gab aba, don haka na shiga dimuwa sosai a lokacin da naga rahoton da wasu marasa mutunci ke watsawa akaina.

“Na san wannan karamin aikin irin yan siyasan nan ne masu ci da zuci, dake neman suna ta hanyar bata ma wani suna, tare da cin mutuncin masu mutunci.” Inji Kashim Gaidam.

A wani labarin kuma, a yau ne babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta gudanar da taron shuwagabanninta domin tattauna matakan daya dace su dauka biyo bayan dage zaben shugaban kasa da hukumar INEC ta yi daga ranar 16 ga wata zuwa ranar 23 ga wata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel