‘Yan bingida sun yi awon gaba da Jigon PDP Emmanuel Agiso a gidan sa

‘Yan bingida sun yi awon gaba da Jigon PDP Emmanuel Agiso a gidan sa

Mun ji labari cewa an sace wani daga cikin manyan jam’iyyar PDP a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin kasar nan yayin da ake shiryawa zaben shugaban kasa da za ayi a karshen makon nan.

‘Yan bingida sun yi awon gaba da Jigon PDP Emmanuel Agiso a gidan sa

An je har gida an sace wani Jigon PDP a Jihar Adamawa
Source: UGC

Wasu ‘yan bindiga ne su ka sace Emmanuel Agiso wanda yana cikin jiga-jigan babban jam’iyyar hamayya watau PDP a jihar Adamawa inda nan ne ‘dan takarar shugaban kasa na PDP watau Alhaji Atiku Abubakar ya fito.

Wadannan ‘yan bindiga sun dura har gidan Mista Emmanuel Agiso ne da ke cikin karamar hukumar Girei da ke kusa da babban birnin Yola na jihar, su kayi gaba da shi. An sace Mista Agiso ne a gaban Iyalan sa a jiya Ranar Litinin.

KU KARANTA: An yi gaba da kudin kamfe a Jam'iyyar APC ta reshen Benuwe

Wani ‘dan uwan wannan babban ‘dan siyasa mai suna Tyros Agiso, ya bayyana ‘yan jarida cewa an sace babban jigon PDP na Adamawa ne a cikin gidan sa da kimanin karfe 1:00 na tsakar dare, ba tare da an taba ko mutum guda a gidan ba.

‘Dan uwan wannan ‘dan siyasa ya sanar da manema labarai cewa wadannan ‘yan bindiga sun shiga gidan Agiso ne da manyan makamai na kare-dangi. Sai dai an yi dace ba su dauki komai ba sai wayar salular Uwargidan wannan mutumi.

Bisa dukkan alamu dai barayin sun dauki wayar Iyalin mutumin ne kuma su ka bar wayar sa a cikin gida saboda ta zama hanyar sadarwar da za a tattauna kudin da za a biya kafin a sake sa. Yanzu dai maganar ta kai gaban ‘yan sanda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel