Olawepo-Hashim ya nemi INEC ta dage zaben Shugaban kasa zuwa nan gaba

Olawepo-Hashim ya nemi INEC ta dage zaben Shugaban kasa zuwa nan gaba

Mun samu labari cewa wani ‘dan takarar shugaban kasar Najeriya a zaben bana a karkashin jam’iyyar hamayya ta PT watau Peoples Trust, ya nemi hukumar zabe ta sake dada dakatar da zaben kasar.

Olawepo-Hashim ya nemi INEC ta dage zaben Shugaban kasa zuwa nan gaba

Gbenga Olawepo-Hashim ya na so a dakatar da zaben 2019 sai an shirya
Source: UGC

Kamar yadda labari ya zo mana daga jaridar nan ta TheCable ta kasar nan jiya, Gbenga Olawepo-Hashim, wanda yake neman kujerar shugaban kasa a 2019, ya rubutawa hukumar INEC wasika cewa ta sake dage zaben bana,

Mista Gbenga Olawepo-Hashim, ya aika takarda ne ta musamman zuwa ga shugaban hukumar INEC mai zaman kan-ta watau Farfesa Mahmood Yakubu, yana mai cewa akwai bukatar a dage zaben gaba daya zuwa nan gaba.

KU KATANTA: Ainihin abin da ya sa INEC ta dakatar da zaben Shugaban kasa a Najeriya

‘Dan takarar yake cewa jigilar kayan aikin zaben zai dauki lokaci sosai don haka yake ganin akwai bukatar hukumar ta INEC ta dakatar da zaben nan da zuwa wani dogon lokaci, a maimakon ayi gaggawar sa ranar da za a gaza.

Olawepo-Hashim yake cewa a na sa ra’ayin ya fi dacewa ga INEC ta zabi lokacin da ta kintsa domin a gudanar da zaben a maimakon tayi garajen maida zaben zuwa mako mai zuwa. Hashim yace yana tsoron abin da za a ji kunya.

‘Dan takarar ya kuma roki shugaban INEC na kasa da ya bari a cigaba da kamfe har sai zuwa daf da lokacin da za a shirya zabe. Tuni dai dama hukumar ta ji kukan ‘yan siyasa ta amince da wannan kira

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel