Zabe: APC ta yi rashin jigo a jihar Bauchi

Zabe: APC ta yi rashin jigo a jihar Bauchi

A yayin da ya rage saura kwanaki kadan a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya, Honarabul Lura Musulmi, jigo a APC, ya fita daga jam’iyyar.

Da ya ke ganawa da manema labarai a otal din Kapool, Honarabul Musulmi, wanda shine mataimakin darektan yakin neman zaben Dalhatu Abubakar, dan takarar kujearar majalisar wakilai a mazabar Dass/Tafawa Balewa/Bogoro, a karkashin tutar jam'iyyar APC ya ce bashi da sha’awar cigaba da zama a cikin jam’iyyar APC har zuwa lokacin zabe.

Kazalika, honarabul Musulmi ya bayyana cewar har yanzu bai yanke shawara a kan jam’iyyar da zai koma ba amma ya ce ya na tuntubar magoya bayan sa a kan hakan.

Zabe: APC ta yi rashin jigo a jihar Bauchi

APC ta yi rashin jigo a jihar Bauchi
Source: UGC

Ba ni da sha’awar cigaba da zama a cikin jam’iyyar APC kuma bani da sha’awar cigaba da kasancewa cikin ma su yi wa dan takarar kujerar majalisar wakilai na Dass/Tafawa Balewa/ Bogoro a APC kamfen. Ina so ku sani cewar na yi hakan ne bisa ra’ayin kai na,” a kalaman honarabulhonarabul Musulmi.

DUBA WANNAN: Dage zabe: Jam’iyyar PDP za ta gudanar da muhimmin taro ranar Talata

Dan takarar kujerar majalisar wakilan a APC, Dahatu Abubakar Kantana, zai fafata ne da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da ke takara a karkashn inuwar jam’iyyar PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel