Fadan manya: Atiku ya shigar da Shugaba Buhari kara kotu, ya nemi diyyar Naira biliyan 2

Fadan manya: Atiku ya shigar da Shugaba Buhari kara kotu, ya nemi diyyar Naira biliyan 2

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya maka shugaba Buhari kotu kan aabun da ya kira rainin hankali.

Fitaccen dan siyasar, Atiku Abubakar dai ya shigar da karar ne yana kalubalantar shugaba Buhari da wata kungiyar dake goyon bayan sa kan rena masa hankali wajen kai shi kara a wata kotu ta daban inda ya bukaci ban hakuri daga gare su da kuma diyyar Naira biliyan 2.

Fadan manya: Atiku ya shigar da Shugaba Buhari kara kotu, ya nemi diyyar Naira biliyan 2

Fadan manya: Atiku ya shigar da Shugaba Buhari kara kotu, ya nemi diyyar Naira biliyan 2
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wasu 'yan Arewa mazauna Legas sun bayyana yadda za suyi

Legit.ng Hausa ta samu cewa tun farko dai wata kungiya dake rajin yada ayyukan da shugaba Buhari yayi a fadin tarayya mai suna Buhari Campaign Organisation ta kai shi dan takarar Atiku kotu tana zargin sa da yiwa shugaba Buhari da iyalan sa kazafi na mallakar bankin Key Stone da kamfanin 9Mobile.

Sai dai shi kuma a karar da ya shigar, ya bukaci kotun data tisaltawa shugaba Buharin ya bashi hakuri sannan kuma ya biya shi diyyar Naira biliyan 2 wadanda yace Naira biliyan 1 a rabawa 'yan gudun hijira, ita kuma dayar Naira biliyan 1 a saka a gyaran makarantun kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel