Ban shawarci Buhari ya hakura da takara ba – IBB

Ban shawarci Buhari ya hakura da takara ba – IBB

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida, ya nesanta kan sa daga wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta a kan cewar ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janye takarar neman tazarce da ya ke yi.

Wata kafar watsa labarai a yanar gizo, Elombah News, ce ta wallafa rahoton da ke cewa tsohon shugaban kasar ya shawarci Buhari ya janye takarar sa domin bawa sabbin jinni dama a wani sako da ya fitar a shafin sa da ke dandalin sada zumunta.

Elomah ta wallafa labarin da ke cewa IBB ya ce; “akwai bukatar mu bawa shugaban kasa Muhammdu Buhari hadin kai domin ya kamala zangon mulkin sa a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2019 tare da shirya yadda za a mika mulki ga sabbin jinni.

“Ina bayar da wannan shawara ne a matsayina na mai ruwa da tsaki a harkokin da su ka shafi Najeriya kuma dan kishin kasa da ke burin ganin kasar sa ta samu cigaba.

Ban shawarci Buhari ya hakura da takara ba – IBB

Buhari da Babangida
Source: UGC

“Ba wai ina da niyyar dakatar da shugaba Buhari daga morar ‘yancin sa na yin takara ba ne amma akwai lokacin da mutum ya dace ya hakura da wani burin na kashin kan sa domin cigaban kasar sa.”

Sai dai a yau, Litinin, ofishin yada labarai na IBB ya bayyana cewar tsohon shugaban kasar ba shi da shafi a dandalin sada zumunta, saboda haka ba shine ya fadi maganganun da ake alakanta su da shi ba.

Tsohon shugan kasa IBB ya lura da cewar ana. yada wani labari daga shafin sada zumunta na Tuwita da ake alakanta wa da shi.

DUBA WANNAN: Dage zabe: Jam’iyyar PDP za ta gudanar da muhimmin taro ranar Talata

“Ofishin yada labarai na tsohon shugaban kasa ya na mai sanar da jama’a, musamman ma’abota amfani da dandalin sada zumunta, su sani cewar IBB bashi da shafi a dandalin Tuwita da kuma dukkan ragowar dandalin sada zumunta.

“Mu na kira ga jama’a da su sani cewar shafin da ke dauke da hotuna da sunan IBB na bogi ne, wasu ne su ka kirlkire shi domin haifar da rudani a tsakanin ‘yan Najeriya,” a cewar jawabin na ofsihin yada labaran Babangida.

Sanarwar ta kara cewa IBB, a matsayin sa na dattijon kasa, ba zai yi abinda ya san kan iya haifar da rudani ko raba kan jama’a ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel