Dage zabe: Cikin fushi, wasu 'yan Najeriya sun fadi matakin da za su dauka ranar zabe

Dage zabe: Cikin fushi, wasu 'yan Najeriya sun fadi matakin da za su dauka ranar zabe

Wasu 'yan kasuwa a Najeriya dake gudanar da sana'o'in su a sassa daban da asalin garin su da kuma suka tafi garuruwan nasu na asali domin yin zabe sun ce ba za su iya tsayawa ba har a gudanar da zabuka ranar 23 ga watan Fabrairu ba.

Ranar Asabar din da ta gabata ne dai wajen karfe 2 na safiyar narar hukumar zaben Najeriya, INEC, ta sanar da dage zabukan kasar da mako daya da tsakar dare, awowi kadan kafin a bude rumfunan zabe.

Dage zabe: Cikin fushi, wasu 'yan Najeriya sun fadi matakin da za su dauka ranar zabe

Dage zabe: Cikin fushi, wasu 'yan Najeriya sun fadi matakin da za su dauka ranar zabe
Source: UGC

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 4

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce sun dage zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya daga ranar 16 ga watan Fabraitru zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.

Ya kara da cewa an dage zaben gwamnoni daga ranar biyu ga watan Maris zuwa ranar tara ga watan na Maris. Lamarin ya bata ran 'yan kasar da ma masu sanya ido da suka je kasar daga kasashen waje.

A wani labarin kuma wasu bayanai da ke fitowa a 'yan awannin da suka gabata sun nuna cewa akwai rabuwar kai da kuma sabanin fahimha a tsakanin shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta kasa watau INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da ministan Sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika.

Mun samu dai cewa shugaban na INEC da yake bayyana dalilan da ya sa hukumar sa ta dage gudanar da zaben shugaban kasa da sati daya, yace hadda matsalolin yanayi da hazo wanda yace ya safi jigilar kayayyakin zaben su ta jiragen sama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel