Daga zabe: Jagorar tawagar sa-ido ta kungiyar ECOWAS ta bar Najeriya

Daga zabe: Jagorar tawagar sa-ido ta kungiyar ECOWAS ta bar Najeriya

Shugabar tawagar sa-ido ta kungiyar ECOWAS a zaben Najeriya, tsohuwar shugabar kasar Laberiya, Ellen Johnson Sirleaf, ta bar Najeriya tare da koma wa kasar ta a yau, Litinin, bayan daga zaben ranar 16 ga watan Fabrairu da hukumar zabe ta kasa (INEC) yi.

Jonatahn Bara-Hart, darektan sadarwa a ECOWAS, ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) hakan ta wayar tarho a yau, Litinin, a Abuja. Ya kara da cewa uwargida Johnson-Sirleaf, za ta dawo Najeriya ranar Alhamis.

Idan kuna Magana ne a kan ma su sa-ido a zabe, zan iya fada ma ku cewar an ba su zabin su zauna zuwa sabuwar ranar da za a gudanar da zabe, da yawan su na nan a Najeriya. Ban sani ba ko wasu sun bar Najeriya.

“Ba na jin uwargida Johnson-Sirleaf za ta bar tawagar ta, watakila za ta dawo ranar Alhamis,” a cewar Mista Bara-Hart.

Daga zabe: Jagorar tawagar sa-ido ta kungiyar ECOWAS ta bar Najeriya

Uwargida Allen Johnson-Sirleaf
Source: Getty Images

Mista Bara-Hart ya ce akwai mutane hudu da su ka fito daga sassan Afrika daban-daban a tawagar uwargida John-Sirleaf.

NAN ta rawaito cewar kungiyoyin United Nation, Commonwealth, European Union, African Union, Organisation of Islamic Cooperation na daga cikin kungiyoyin da hukumar zabe (INEC) ta amince da su domin sa-ido a zabukan da za a yi a kasar nan.

DUBA WANNAN: Dage zabe: Jam’iyyar PDP za ta gudanar da muhimmin taro ranar Talata

A ranar Asabar, 16 ga watan Fabarairu, ne INEC ta daga zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya zuwa ranar Asabar, 23 ga wata. Kazalika, INEC ta daga zaben gwamnoni da ‘yan majilasar dokoki daga ranar 2 ga watan Maris zuwa ranar 9 ga wata.

A ranar Asabar din ne gamayyar kungiyoyin sa-ido a zaben Najeriya su ka fitar da wata sanarwa a kan bukatar INEC ta mayar da hankali domin ganin cewar an gudanar da zabuka a sabbin lokutan da ta ambata.

Gamayyar kungiyoyin sun bayyana cewar za su cigaba da sa-ido a kan shirye-shiryen da hukumar zabe ke yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel