Gwamnatin Kaduna da Bankin duniya zasu gina babban kamfanin sarrafa citta

Gwamnatin Kaduna da Bankin duniya zasu gina babban kamfanin sarrafa citta

Gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana shirye shirye sun yi nisa tsakaninta da gwamnatin tarayya da bankin duniya wajen kafa wani katafaren kamfanin sarrafa citta na zamani a karamar hukumar Kachia ta jahar Kaduna.

Legit.ng ta ruwaito jami’in watsa labaru na ma’aikatan noma da gandun dazuka, Malam Dahiru Abdullahi ne ya bayyana haka a ranar Litinin a garin Kaduna, inda yace gwamnatin jahar ta ribaci tsarin sarrafa kayan noma, inganta ayyuka da inganta rayuwa, (APPEALS), na bankin duniya ne wajen wannan aiki.

KU KARANTA: Yan bindiga sun tashi kauyuka 17, sun kashe 5, sun yi garkuwa da 35 a jahar Neja

A jawabinsa, Abdullahi yace manufar shirin shine samar da sabon cibiyar sarrafa citta, tare da farfado da sauran tsofaffin kamfanonin dake sarrafa citta a jahar Kaduna, wanda yace idan aka kammala aikin zasu samar da dimbin ayyuka ga matasan jahar, musamman ma yan karkara.

“Zuwa yanzu gwamnatin jahar ta bayar da kudin fara aiki na naira miliyan 48 ga APPEALS, haka zalika za’a farfado da kamfanin sarrafa citta na Kachia wanda ya daina aiki tun a shekarar 2003 don taimaka ma manoman citta sarrafa abinda suka noma.

“Nan gaba kadan kwararru zasu gudanar da bincike tare da tattara rahoto akan yadda za’a tsara noman zamani na citta a yankin Kachia, kamar yadda ake yi a kasashen da suka cigaba, hakan zai baiwa jahar damar shiga cikin sahun kasashen dake fitar da citta a duniya.

“A duk fadin Najeriya a Kaduna kadai ake noma cittan da za’a iya sayarwa, kuma citta ne wanda aka yi ittifakin yafi kowanne kyau a Duniya, amma matsalar rashin amfani da hanyoyin noman zamani da kuma rashin kayan aikin sarrafashi yasa baya yin darajar daya kamata.” Inji shi.

Daga karshe Dahiru yace tuni gwamnatin jahar ta samar da wani waje a garin Assako karamar hukumar Kachia da za’a dinga shuka dashen cittan, tare da kayan aikin tsaftace cittan, duk a kokarinta na samar da wannan kamfani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel