Dage zabe ya sa dala ta karye warwas a Najeriya

Dage zabe ya sa dala ta karye warwas a Najeriya

Rahotanni da ke billowa sun nuna cewa ana kara samun yawan dalolin Amurka inda yawo cikin kasuwar musayar kudade a jihohin Lagas da Kano da Kaduna da kuma Port Harcourt.

Hasashe sun nuna cewa mafi yawan dalolin da ke yawo dai, na fitowa ne daga hannun 'yan siyasa da ke neman naira.

Tuni dai yawaitar dalar ta karya farashinta.

Dage zabe ya sa dala ta karye warwas a Najeriya

Dage zabe ya sa dala ta karye warwas a Najeriya
Source: UGC

An tattaro cewa zuwa yanzu 'yan siyasa masu hannu da shuni, musamman wadanda suka tara dalolin Amurka sun bazama cikin kasuwannin chanji inda suke neman naira ido rufe.

Ana zargin 'yan siyasa na neman nairar ne saboda rarrabawa magoya bayansu da sauran 'yan siyasa masu fada a ji a lokacin kamfe ko kuma a lokacin gudanar da babban zabe na shugaban kasa a kasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: INEC ta amince da ci gaba da kamfen din siyasa

A wani labari na daban, mun ji cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC reshen jihar Neja, ta karbe tikitin takarar kujerar wakilin shiyyar Neja ta Gabas na majalisar dattawa daga hannu Sanata David Umaru ta kuma danka shi a hannun Muhammad Sani Musa.

Sauya sunan dan takarar da hukumar INEC ta yi ya biyo bayan hukuncin babbar kotun tarayya, da ta tabbatar da Sani Musa a matsayin wanda ya yi nasarar samun tikitin takara a zaben fidda gwani da aka gudanar yayin da babban zaben kasa ke kan gaba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel