Ba na tsoron faduwa zabe - Buhari

Ba na tsoron faduwa zabe - Buhari

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ba ya da wata fargaba ko shayi na faduwa a babban zaben kujerar shugaban kasa da za a gudanar a ranar Asabar, 23, ga watan Fabrairun 2019.

Majaiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya bayyana hakan ne yayin taron jiga-jigan jam'iyyar sa ta APC da aka gudanar a yau Litinin cikin babbar hedikwatar jam'iyyar da ke garin Abuja.

Buhari yayin taron sa na yakin neman zabe a jihar Bayelsa

Buhari yayin taron sa na yakin neman zabe a jihar Bayelsa
Source: Facebook

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, ganawar shugaban kasa Buhari tare da kusoshin jam'iyyar sa ta gudana ne a sakamakon hukuncin dage babban zaben kasa da hukumar INEC ta yi a ranar Asabar ta makon da ya gabata.

Manyan jiga-jigai da suka halarci taron sun hadar shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar, Bola Tinubu, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da kuma gwamnoni 11 na jam'iyyar.

KARANTA KUMA: Shiyyar Neja ta Gabas: INEC ta karbe tikitin takarar Sanata Umaru ta bai wa Sani Musa

Cikin kalami nasa da tabbatar da rashin faragabar sa ta samun nasara, shugaban kasar yake cewa ya girgiza magoya bayan sa yayin yawon sa na shawagi da yakin neman zabe cikin garin Abuja da kuma jihohi 36 da ke fadin kasar nan.

Da ya ke ci gaba da jaddada kudirin sa na kare martabar al'ummar kasar nan, shugaba Buhari ya yi kira da su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri'un su daidai da ra'ayoyin su a ranakun zabe kamar yadda hukumar INEC ta kayyade.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel