An Cafke mutum 4 da ke da hannu a kisan shugaban PDP a jihar Cross River

An Cafke mutum 4 da ke da hannu a kisan shugaban PDP a jihar Cross River

An cafke wasu mutane 4 da ake zargi da hannu a kisan shugaban jam'iyyar PDP na mazaba a yankin Bendeghe Ekiem na karamar hukumar Etung na jihar Cross River mai suna Mista Ayuk Ogar.

Wata majiya ta bayyana mana cewa Mista Ogar da wasu wadanda aka kashe tare da shi a ranar Asabar din da ta gabata a Bendeghe, sun mutu ne a wata fafatawar harbi in harba tsakanin magoya bayan jam'iyyar PDP da APC.

Fafatawar ta afku ne jim kadan bayan shugabannin jam'iyya a yankin sun sanya hannu a kan takardar kudirin zaman lafiya don tabbatar da gudanar da zabuka cikin kwanciyar hankali.

An rawaito cewa dai wasu da dama sun samu raunika a dambaruwar kuma a halin yanzu suna karbar kulawa a wajen likitoci a babban asibitin Ikom. 

KU KARANTA: Jawabin Buhari kan masu kwace akwatin zabe: Ba zamu yarda ba - PDP

Wani jigon jam'iyyar PDP kuma hadimin gwamna Ben Ayade kan noman Cocoa, Mista Oscar Ofuka, ya bayyana cewa rikici tsakanin tawagogin biyu ya fara ne bayan da jam'iyuun APC da PDP suka kammala rattaba hannu akan kudirin zaman lafiya tsakanin jam'iyyun.

Mista Ofuka ya ci gaba da cewa, magoya bayan APC wadanda ke dauke da bindugu da adduna basu gamsu da kudirin na zaman lafiya ba, inda basu yi wata-wata ba sai suka budewa magoya bayan PDP wuta da basa dauke da makamai.

"Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu dai akwai Mista Ayuk Ogar, shugaban jam'iyyar PDP na mazabar Bendeghe Ekiem. kuma hakan ya jefa mazauna kauyen cikin tashin hankali, inda suke rokon gwamnati da ta gaggauta samar da tsaro a yankin don tabbbatar da tsaro ga lafiya, rayuka da dukiyar al'umma." Yace.

Sai dai kuma jami'in hulda da jama'a na jam'iyyar APC na jihar, Mista Bassey Ita, ya musanta zargin cewa magoya bayan jam'iyyarsa ne suka aikata kashe-kashen.

Ya ce, " Ba gaskiya bane. Duk wanda ya fada maka cewa APC ce ta haddasa rikicin yana fadin ra'ayinsa ne kawai don cimma wata bukata ta siyasa."

"Muna so muyi amfani da wannan dama wajen jan hankali gwamna Ben Ayade da ya guji aikata abubuwan da zu dumama yaayin siyasa a jihar don gudun haddasa fitana a fadin jihar."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin. Sai dai ta ce mutane biyu ne kadai suka mutu. 

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel