Yadda Shugaban INEC yake yi wa Jam’iyyar PDP aiki a 2019 – Amaechi

Yadda Shugaban INEC yake yi wa Jam’iyyar PDP aiki a 2019 – Amaechi

Yayin da ake shirin zabe a Najeriya, mun ji cewa Ministan sufuri na kasar watau Rotimi Amaechi, ya zanta da ‘yan jarida inda ya tattauna a kan batutuwa da-dama wanda su ka hada da zaben kasar.

Yadda Shugaban INEC yake yi wa Jam’iyyar PDP aiki a 2019 – Amaechi

Amaechi ya bayyana alakar Hukumar INEC da Gwamnan Ribas
Source: Depositphotos

Rotimi Amaechi yayi hira da ‘yan jarida yana mai zargin shugaban hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta, Farfesa Mahmood Yakubu da hada baki da manyan jam’iyyar PDP irin su Nyesom Wike domin a kawowa APC cikas.

Tsohon gwamnan na Ribas yake cewa shi ba mutum bane mai neman rikici don haka yace ba za su tada rikici don hukumar zabe na kasa watau INEC ta ki ba jam’iyyar APC dama ta tsaida ‘yan takarar majalisa a jihar Ribas ba.

Duk da matsalar da jam’iyyar APC ta samu a Ribas, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa mutanen jihar za su zabi shugaba Buhari a Ranar Asabar, sannan kuma su na sa rai INEC ta sake shawara ta ba APC dama ayi zaben da su.

KU KARANTA: PDP ta nemi a binciki ingancin na’urorin Card Readers kafin zabe

Ministan kasar yake cewa gwamna Nyesom Wike yana amfani da Magnus Abe na jam’iyyar APC mai mulkin kasar ne wajen ganin an hana APC shiga zaben 2019. Ministan yace INEC da kan ta kuma tana yi wa PDP aiki ne.

Mista Rotimi Amaechi yake cewa Mahmood Yakubu yana yi wa Wike aiki ne domin kuwa akwai alaka tsakanin su tun lokacin da shugaban na INEC yake rike da hukumar TETFund, a sa’ilin da Nyesom Wike yake Ministan ilmi.

Babban Ministan ya zargi gwamnan jihar ta sa da kokarin dawo da siyasar daba inda ya kuma ce Sanata Magnus Abe da Nyesom Wike sun yi yarjejeniyar za su taimakawa juna a zaben da za ayi domin ganin Buhari ya sha kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel