Yanzu Yanzu: INEC ta amince da ci gaba da kamfen din siyasa

Yanzu Yanzu: INEC ta amince da ci gaba da kamfen din siyasa

- Hukumar zabe ta amince da ci gaba da kamfen din siyasa

- An tattaro cewa hukumar ta amince da hakan ne biyo bayan yawan korafe-korafe da ta samu daga jam'iyyun siyasa mussamman manyan jam'iyyun kasar guda biyu

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta amince da ci gaba da kamfen din siyasa.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa daga kwamishinan zabe na kasa kuma Shugaban kwamitin masu wayar da kan masu zabe, Mista Festus Okoye ya bayyana hakan a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu.

An tattaro cewa hukumar ta amince da hakan ne biyo bayan yawan korafe-korafe da ta samu daga jam'iyyun siyasa mussamman manyan jam'iyyun kasar guda biyu wato APC da PDP da suka nemi a bari su ci gaba da kamfen tunda dai an dage zaben.

Yanzu Yanzu: INEC ta amince da ci gaba da kamfen din siyasa

Yanzu Yanzu: INEC ta amince da ci gaba da kamfen din siyasa
Source: Instagram

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin tayar da tarzoma a ranan zabe da cewa su nisanci akwatunan zabe ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

A wata ganawar gaggawa da jigogin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sukayi ranan Litinin a birnin tarayya Abuja, shugaban kasa ya ce duk wanda ya tayar da rikici musamman ta hanyar daukan akwatin zabe, to abkin ransa.

KU KARANTA KUMA: Ina iya rantsewa da Qur’ani cewa INEC ta sanar da PDP batun dage zabe - Oshiomhole

Buhari yayi wannan jawabi ne bayan ya caccaki hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta wato INEC kan dage zabe daga ranan 16 ga Febrairu zuwa 23 ga watan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel