Dage zabe: Jam’iyyar PDP za ta gudanar da muhimmin taro ranar Talata

Dage zabe: Jam’iyyar PDP za ta gudanar da muhimmin taro ranar Talata

A gobe, Talata, ne jam’iyyar PDP za ta gudanar da taron shugabannin ta na kasa (NEC) kamar yadda sakataren jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, ya fitar da sanarwa.

Taron na zuwa ne bayan hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta daga zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da ta shirya gudanar wa ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, zuwa ranar Asabar, 23 ga watan Fabarairu.

Mista Ologbondiyan ya bayyana cewar za a yi taron ne a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja da misalign karfe 12:00 na rana.

Dage zabe: Jam’iyyar PDP za ta gudanar da muhimmin taro ranar Talata

Kola Ologbondiyan
Source: Depositphotos

Daga cikin wadanda ake tsammanin za su halarci taron akwai gwamnonin jam’iyyar da kuma kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) da sauran su.

DUBA WANNAN: Yariman kasar Saudiyya ya warware zare da abawa a kan rahoton sayen Manchester

Duk da jam’iyyar ba ta bayyana abinda za ta tattauna a wurin taron ba, majiyar mu ta bayyana ma na cewar batun daga zaben shugaban kasa da ‘yan takarar majalisar tarayya ne zai fi daukan hankali mahalarta taron.

A yau, Litinin, ne jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da nata taron domin tattauna batun daga zaben da INEC ta yi ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel