Jawabin Buhari kan masu kwace akwatin zabe: Ba zamu yarda ba - PDP

Jawabin Buhari kan masu kwace akwatin zabe: Ba zamu yarda ba - PDP

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta siffanta jawabin shugaba Muhammadu Buhari inda ya umurci jami'an soji da yan sanda cewa kada su dagawa kowa kafa idan yayi kokarin tayar da hayaniya a ranan zabe a matsayin umurnin kisan kai zalla.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin tayar da tarzoma a ranan zabe da cewa su nisanci akwatunan zabe ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

A wata ganawar gaggawa da jigogin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sukayi ranan Litinin a birnin tarayya Abuja, shugaban kasa ya ce duk wanda ya tayar da rikici musamman ta hanyar daukan akwatin zabe, to abkin ransa.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP za ta gudanar da muhimmin taro ranar Talata

Amma wannan abu bai yiwa jam'iyyar adawa ta PDP dadi ba inda kakakin jam'iyyar Kola Ologbodiyan ya saki jawabin cewa wannan jawabi da Buhari yayi barazanace ga rayuwar yan Najeriya da kuma kokarin kawar da hankalin mutane kan tuggun da suke shiryawa a boye.

Yace: "Muna kyautata zaton cewa wannan kira da shugaba Buhari yayi ba kokarin amfani da wasu sojojin karya bane da APC ta shirya domin kisan yan Najeriya, kwace akwatunan zabe da gudanar da magududinsu ranar zabe.

"Wannan umurni ce na kisa, wacce bai kamata ta fito daga harshen shugaban wata kasa a duniya ba. Muna kira ga yan Najeriya da kasashen wajen su rike Buhari alhaki idan wani rikici ya faru ranan zabe."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel