Sai da INEC ta sanar dda PDP kafin dage zabe - Oshiomole

Sai da INEC ta sanar dda PDP kafin dage zabe - Oshiomole

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta wato INEC da ma'aikatanta sun sanar da babban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP, shirin dage zabe.

Oshiomole yace sai da INEC ta fadawa PDP kafin ta dage zaben ranan Asabar. Ya bayyana hakan ne a ganawar gaggawa da shugabannin jam'iyyar APC sukayi ranar Litinin a birnin tarayya Abuja.

Tsohon gwamnan jihar Edo yace: "Zan iya rantsewa da Al-Qur'ani cewa INEC da ma'aikatanta sun sanar da Peoples Democratic Party, PDP, kafin dage zabe. PDP na sane da dukkan abinda ke faruwa na shirin dage zaben."

"Shi yasa labarin bai zo musu da mamaki ba. Sai suka zamar da mu tamkar wawaye saboda muna can muna ta shirye-shiryen zabe su kuma suna kwance."

KU KARANTA: Jawabin Buhari kan masu kwace akwatin zabe: Ba zamu yarda ba - PDP

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin tayar da tarzoma a ranan zabe da cewa su nisanci akwatunan zabe ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

A wata ganawar gaggawa da jigogin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sukayi ranan Litinin a birnin tarayya Abuja, shugaban kasa ya ce duk wanda ya tayar da rikici musamman ta hanyar daukan akwatin zabe, to a bakin ransa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel