Zabe: INEC ta gargadi 'yan Najeriya a kan dogaro da sakamako ta kafafen sada zumunta

Zabe: INEC ta gargadi 'yan Najeriya a kan dogaro da sakamako ta kafafen sada zumunta

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ja kunnen jama’a da su guje ma amfani da sakamakon zabe da ake yadawa a kafafen sada zumunta, maimakon haka su jira ingantaccen sakamako daga bakin hukumar zaben.

Hukumar ta yi wannan gargadi ne a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu a Birnin Kebbi, babbar birnin jihar Kebbi.

Kwamishinan zabe na jihar Kebbi, Alhaji Ahmad Mahmud ne ya yi wannan jan kunnen a yayinda yake zantawa da masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe a jihar.

Zabe: INEC ta gargadi 'yan Najeriya a kan dogaro da sakamako ta kafafen sada zumunta

Zabe: INEC ta gargadi 'yan Najeriya a kan dogaro da sakamako ta kafafen sada zumunta
Source: Instagram

"Labaran bogi ya zama ruwan dare yanzu, kuma ba karamin barazana bane ga kokarin hukumar mu na tabbatar da an gudanar zabukka masu inganci, don haka dole sai kun yi hankali da kafafen sada zumunta, kada ku saurari wani sakamakon zabe in dai ba daga hukumar zabe ya fito ba,"Inji Mahmud

Mahmud ya kara da cewa; "Jami’an INEC na jihohi ne kadai suke da hurumin fadin sakamakon zabe a kananan hukumomi da matakin jiha, duk wata sanarwa da ba daga hukumar bane, to ayi watsi da shi, zuwa yanzu mun raba katin zabe 1,938,171, inda aka amshi 1,860,239, har yanzu akwai 77,932 suna nan ba a karba ba."

KU KARANTA KUMA: Ina iya rantsewa da Qur’ani cewa INEC ta sanar da PDP batun dage zabe - Oshiomhole

A wani amari na daban, mun ji cewa babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi bayani da kuma Karin haske game da umurnin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba hukumomin tsaro a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu.

Tinubu wanda yayi magana bayan taron shugabannin APC a Abuja, inda Shugaban kasa ya bayar da umurnin cewa ayi maganin masu satar akwatin zabe yayinda kasar ke shirye-shiryen zabenta da aka dage.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel