Waiwaye: Furucin Buhari bayan dage zaben 2015

Waiwaye: Furucin Buhari bayan dage zaben 2015

A ranar Asabar, 16, ga watan Fabrairun 2019, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta bayar da sanarwar dage babban zabe na kujerar shugaban kasa da kuma na 'yan majalisun tarayya zuwa ranar Asabar ta wannan mako.

Ko shakka ba bu tarihi ya tabbatar da cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi babatu na caccakar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, a yayin da ta dage babban zaben kasa na shekarar 2015 da ta gabata.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, kazalika shugaban kasa Buhari wanda ya yi takara a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC ya kuma yi suka gami da caccakar gwamnatin baya ta tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan na jam'iyyar adawa ta PDP.

Buhari yayin kada kuri'ar sa a zaben 2015 cikin garin Daura

Buhari yayin kada kuri'ar sa a zaben 2015 cikin garin Daura
Source: UGC

A ranar 8 ga watan Fabrairun 2015, kwanaki shida gabanin gudanar da zaben kasa, hukumar INEC ta dage zaben kujerar shugaban kasa na ranar 14 ga watan Fabrairu zuwa tsawon makonni shida tare da bayar da dalilai na rashin tsaro da kasar ke fuskanta a wancan lokaci.

Tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya bayar da dalilai na barazanar rashin tsaro da suka sanya hukumar sa ta dakatar da zaben zuwa ranar 28 ga watan Maris a shekarar ta 2015.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari cikin fushi ya yi tur gami da Allah wadai dangane da hukuncin da hukumar INEC ta dauka na dage babban zaben a wancan lokaci sakamakon dalilai na rashin tsaro da ta wassafa.

KARANTA KUMA: Sojin kasan Najeriya sun hallaka masu garkuwa da mutane 37, sun ceto Mutane 80 a jihar Zamfara

Cikin kalami nasa yayin ganawa da manema labarai, shugaba Buhari ya ce, yayin da Najeriya ke kunshe da kananan hukumomi 774, rashin tsaro a kananan hukumomi 14 ba ya da wata madogara ta za ta sanya a dage babban zabe na kasa.

Yayin tambayar manema labarai "me a kayi a kayi wata Boko Haram", ya kuma buga misali dangane da yadda rashin tsaro na mafi tsananin ta'addanci bai hana gudanar da zabe ba a kasar Syria, Pakistan da kuma Afghanistan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel