‘Yan fashi sun shiga cikin gidan Kevin Prince Boateng a Barcelona

‘Yan fashi sun shiga cikin gidan Kevin Prince Boateng a Barcelona

- An burma gidan ‘Dan wasa Kevin Prince Boateng a Ranar Asabar da ta gabata

- ‘Yan fashi sun rutsa gidan Boateng ne a lokacin yana bugawa Barcelona wasa

- Kwanan nan ne kungiyar ta kasar Sifen ta karbo aron ‘Dan wasa Prince Boateng

‘Yan fashi sun shiga cikin gidan Kevin Prince Boateng a Barcelona

Barayi sun auka gidan Prince Boateng a Yankin Kataloniya
Source: Getty Images

Mun samu labari cewa wasu barayi sun dura gidan fitaccen ‘dan wasan Barcelona Kevin Prince Boateng a Ranar Asabar 16 ga watan nan na Fubrairu. An kutsa gidan Tauraron ne a daidai lokacin da yake bugawa kungiyar sa wasa.

Kamar yadda labari ya zo mana, barayin sun auka gidan na sa ne wanda yake cikin unguwar Sarria a Birnin Barcelona. An kuma yi rashin dace an yi awon gaba da dukiyar da ta haura £250,000 na daga tsabar kudi da wasu abubuwan.

KU KARANTA: Ana binciken 'dan wasa Arda Turan bayan yayi dambe a gidan rawa

Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an shiga gidan ‘dan wasan kwallon na Nahiyar Afrika, amma har yanzu dai ba a iya kama kowa da zargin wannan mummunan laifi ba kamar yadda rahoto ya zo mana daga jaridar UK ta kasar Ingila.

Yayin da ake yi wa tsohon ‘dan wasan na kungiyar AC Milan wannan barna, yana can su na fafatawa da kungiyar Real Valladolid a gasar La-ligan Sifen. Barcelona ta yi sa’ar samun galaba a kan kungiyar ne da ci daya rak mai ban haushi.

‘Dan wasan gaban Kevin Prince Boateng na kasar Ghana ya taba bugawa kungiyar AC Milan da Sasulo a kasar Italiya kafin ya dawo Barcelona a matsayin ‘dan wasan aro. ‘Dan wasan ya maye gurbin Munir El haddadi ne wanda ya tashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel