Ina iya rantsewa da Qur’ani cewa INEC ta sanar da PDP batun dage zabe - Oshiomhole

Ina iya rantsewa da Qur’ani cewa INEC ta sanar da PDP batun dage zabe - Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), da jami’anta da bayyanawa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) labarin shirye-shiryen dage zaben shugaban kasa da na yan majalisa, kafin aiwatar da hakan.

Oshiomhole yayi maganan ne a taro na gaggawa da jiga jigan jam’iyyar APC suka gudanar a Abuja a yau Litinin, 18 ga watan Fabrairu bayan dage zabbuka da aka yi.

Tsohon gwamnan na jihar Edo yace, “ina iya daura hannuna a Qur’ani in rantse cewa hukumar INEC da jami’anta sun sanar da jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Shirinta kafin dage zabe.

Ina iya rantsewa da Qur’ani cewa INEC ta sanar da PDP batun dage zabe - Oshiomhole

Ina iya rantsewa da Qur’ani cewa INEC ta sanar da PDP batun dage zabe - Oshiomhole
Source: Twitter

“Yan jam’iyyar PDP na sane da shirye-shiryen tafiyar da zabbukan, wannan ne yasa labarin zaben bai girgiza su ba. Sun maishemu wayaye, saboda mun dage da shirye-shiryen zabbuka yayinda suke walawarsu”.

KU KARANTA KUMA: An samu rabuwar kai a APC reshen Benue kan kudaden kamfen din shugaban kasa

A wani lamari makamancin haka, mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin tayar da tarzoma a ranan zabe da cewa su nisanci akwatunan zabe ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

A wata ganawar gaggawa da jigogin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sukayi ranan Litinin a birnin tarayya Abuja, shugaban kasa ya ce duk wanda ya tayar da rikici musamman ta hanyar daukan akwatin zabe, to abkin ransa.

Buhari yayi wannan jawabi ne bayan ya caccaki hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta wato INEC kan dage zabe daga ranan 16 ga Febrairu zuwa 23 ga watan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel