Rikici, rashin sanin aiki da sauran dalilan da su ka sa aka dage zabe

Rikici, rashin sanin aiki da sauran dalilan da su ka sa aka dage zabe

Mun samu labari daga jaridar The Cable game da ainihin abin da ya sa aka dage zaben da aka shirya za a gudanar a karshen makon da ya gabata. Dole dai aka dakatar da zaben shugaban kasar zuwa makon gobe.

Rikici, rashin sanin aiki da sauran dalilan da su ka sa aka dage zabe

Rahin kwarewar INEC yana cikin abin da ya sa aka dage zabe
Source: Original

Daga cikin matsalolin da aka samu akwai rashin kwarewar aiki na jami’an hukumar INEC. Bayan wannan kuma hukumar tayi fama da matsalar rashin jituwa da yadda da juna tsakanin manyan ma’aikatar hukumar zaben na kasa.

Majiyar jaridar ta bayyana mana cewa har an ta kai ana daf da zaben, wasu kwamishononin na INEC ba su magana da juna. Wannan rikicin cikin gidan ne da kuma matsalar jigilar kaya da rashin tsari yayi tasiri wajen dakatar da zaben.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta na da wasu bukatu na musamman a gaban INEC

Wani babba a hukumar INEC ya fadawa ‘yan jarida cewa a kan tanadi kayan zabe tun ana saura kusan makonni 2 zabe, amma wannan karo babu alamun shiri kamar yadda aka saba. Hakan ya nuna rashin jagoranci a cikin tafiyar hukumar.

Haka zalika, hukumar tayi kokarin shirya zaben a Ranar Litinin, amma hakan ya ki yiwuwa domin kuwa akwai bukatar a sake canza tsarin na’urorin da ake amfani da su wajen tantance masu kada kuri’a wanda zai dauki kusan mako guda.

KU KARANTA: Duk wanda yayi yunkurin sace akwatin zabe a bakin ran sa - inji Buhari

Daga cikin cikas din da aka samu wajen gudanar da zaben shi ne canzawa Amina Zakari wurin aiki da aka yi saboda surutun jama’a daga ofishin gudunarwa inda aka maye gurbin ta da wani Okechukwu Ibeanu wanda bai san kan aiki ba.

An kuma samu matsalar rashin daukar mataki cikin gaggawa inda aka dauki lokaci ba a sanar da Najeriya game da halin da ake ciki ba. Taron da INEC tayi ya kai har cikin dare wanda sai daga baya ne jama’a su ka ji labarin dage zaben.

Manyan kwamishinonin hukumar zaben mai zaman kan-ta sun fahimci cewa dole a dakatar da zaben ganin cewa kayan aiki ba su isa jihohi da-dama ba a Ranar Juma'a. Yanzu dai sai mako mai zuwa za a yi zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel