Sojin kasan Najeriya sun hallaka masu garkuwa da mutane 37, sun ceto Mutane 80 a jihar Zamfara

Sojin kasan Najeriya sun hallaka masu garkuwa da mutane 37, sun ceto Mutane 80 a jihar Zamfara

Da sanadin kafar wata labarai ta Channels TV mun samu cewa, rundunar sojin kasa ta Najeriya ta yi asarar dakaru shida yayin wata musayar wuta da 'yan ta'adda a garin Bini da ke karkashin karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

A yayin wannan lamari na batakashi, rundunar sojin ta samu nasarar hallaka kimanin mutane 37 da ake zargin su da ta'addanci na masu garkuwa da mutane yayin da kuma ta samu nasarar ceto Mutane 80 da suka yi garkuwa da su.

Sojin kasan Najeriya sun hallaka masu garkuwa da mutane 37, sun ceto Mutane 80 a jihar Zamfara

Sojin kasan Najeriya sun hallaka masu garkuwa da mutane 37, sun ceto Mutane 80 a jihar Zamfara
Source: Twitter

Kakakin rundunar sojin kasa mai atisayen Sharan Daji, Manjo Clement Abiade, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai na Channels TV a yau Litinin cikin birnin Gusau.

Manjo Abiade ya bayyana cewa, cikin jerin Mutane da rundunar sojin ta samu nasarar cetowa sun hadar har da Mata da kuma kananan Yara yayin sintiri cikin dajin Dumburum a tsakanin ranar 4 da 14 na watan Fabrairun 2019.

KARANTA KUMA: Najeriya ta dukurkushe gabanin zuwan Buhari - Boss Mustapha

Cikin sanarwar da majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito da sanadin kafar watsa labarai ta Channels TV a yau Litinin, rundunar sojin ba bu zato ba bu tsammani ta yi gamo da 'yan ta'adda bayan dawowar ta daga wani aikin sintiri.

A yayin da jihar Zamfara ke ci gaba da fuskantar kalubale na ta'addanci masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu, kazalika rundunar sojin ta samu nasarar cafke wasu 'yan ta'adda shida a sansanin su tare da muggan makaman su na kare dangi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel