An bukaci hukumar INEC da ta tsige jami’anta da ke da hannu a matsalar da aka samu wajen sarrafa kayanta

An bukaci hukumar INEC da ta tsige jami’anta da ke da hannu a matsalar da aka samu wajen sarrafa kayanta

Wani kwararre a harkar tsaro mai suna Capt. John Ojikutu mai ritaya, yace mai yiwuwa kashi 60 na jami’an hukumar INEC da ke da hannu cikin lamari da yayi sanadiyan dage zaben na a cikin tsarinn har yanzu.

“Lokaci yayi da za’a tantance su sannan a sauke su daga tsarin,” a cewar Ojikutu yayinda yake bayyana ra’ayinsa akan dage zaben kasar da hukumar INEC tayi.

A cewar shi, daga 2011, 2015 da 2019, dalilin da yasa ake daga zabe ba komai bane illa matsalar sarrafa kayayyakin zabe.

An bukaci hukumar INEC da ta tsige jami’anta da ke da hannu a matsalar da aka samu wajen sarrafa kayanta

An bukaci hukumar INEC da ta tsige jami’anta da ke da hannu a matsalar da aka samu wajen sarrafa kayanta
Source: UGC

Yace, “ idan kuka tuna baya daga shekarar 2011 a lokacin Jega , matsalar sarrafa kayan aiki ake yawan samu. Shin hukumar INEC bata koyi darasi ba na zabukan baya har da zaben 2015 da ya gudanar?

”Ba za a rasa kasa da kashi 60 na irin wadannan matsalolin ba a tsarin hukumar; su waye masu kulawa da ayyukan sarrafa kayan aikin hukuman a baya kuma su nawa ne suke a cikin tsarin har yanzu?

KU KARANTA KUMA: An samu rabuwar kai a APC reshen Benue kan kudaden kamfen din shugaban kasa

“Akwai masaniya kwararru akan kowanne banda kwarewan baya? Menene hukumar INEC tayi don cimma wadanannan kwarewan?

"Mai yiwuwa wadanda suka rage a tsarin sun kasance daga cikin kwararru na baya masu hannu cikin tsarin; me zai hana hukumar INEC tantance su sannan ta sauke su." inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel