Da duminsa: Buhari ya yi barazana ga shugaban INEC, Mahmud Yakubu

Da duminsa: Buhari ya yi barazana ga shugaban INEC, Mahmud Yakubu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi barazanar hukunta shugaban hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta, farfesa Mahmoud Yakubu, bayan kammala zaben 2019 da aka dage daga ranan 16 zuwa 23 ga watan Febrairu 2019.

Buhari ya jaddada maganar shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC, Adams Oshiomole, cewa shugaban INEC ya hada baki da jam'iyyar PDP wajen dage zaben 2019 ta hanyar sanar da su kafin sauran al'umman kasa.

Buhari yace: "Sai da na dawo Abuja da wuri saboda misalin karfe 5:30 na asuba aka fada min... Na fadawa mutane cewa mun baiwa INEC dukkan abinda suka bukata."

"Bayan zabe, sai INEC tayiwa yan Najeriya bayani. Sai sun fada mana abinda ya faru. Wajibi ne ayi bayani filla-filla kan abinda ya faru. Ba zan fadi komai fiye da hakan ba a yanzu."

Bayan jawabin shugaba Buhari, an bukaci yan jarida su fita daga cikin dakin taron saboda yan jam'iyyar za suyi tattaunawan sirri.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel