Yanzu-yanzu: Duk wanda yayi yunkurin kwace akwatin zabe, to a bakin ransa - Buhari

Yanzu-yanzu: Duk wanda yayi yunkurin kwace akwatin zabe, to a bakin ransa - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin tayar da tarzoma a ranan zabe da cewa su nisanci akwatunan zabe ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

A wata ganawar gaggawa da jigogin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sukayi ranan Litinin a birnin tarayya Abuja, shugaban kasa ya ce duk wanda ya tayar da rikici musamman ta hanyar daukan akwatin zabe, to abkin ransa.

Buhari yayi wannan jawabi ne bayan ya caccaki hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta wato INEC kan dage zabe daga ranan 16 ga Febrairu zuwa 23 ga watan.

Ya jaddada cewa gwamnati ta baiwa hukumar INEC dukkan abubuwan da suka bukata domin gudanar da zabe cikin sauki amma duk da hakan sun nuna rashin kwarewarsu kuma sun baiwa yan Najeriya kunya.

KU KARANTA: Buhari, Osinbajo, gwamnonin APC sun dira taron gaggawa kan dage zaben INEC

Yace: "Ba zan taba yin amfani da karfina wajen magudin zabe ba. Ba na bukatan haka. Ba zan rainawa yan Najeriya wayo ba. Muna son zaben da zai bari yan Najeriya su zabi wanda sukaso cikin yanci.

Na tafi dukkan sassan kasar nan kuma da abinda na gani, ba ni bukar magudi...... duk wata jiha ko gungun mutane da suke tunani zasu iya tayar da rikici a wannan zabe, to a bakin rayukansu."

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) akalla 11 sun dira sakatariyar jam'iyyar dake birnin tarayya Abuja domin halartan taron gaggawa kan dage zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel