Da dumi-dumi: Oshiomhole na so ayi sauyi a INEC

Da dumi-dumi: Oshiomhole na so ayi sauyi a INEC

- Shugaban APC na kasa Adams Oshiomhole ya bukaci INEC da ta sauya wasu daga cikin manyan jami’anta

- Oshiomhole ya zargi wasu kwamishinonin INEC da aiki tare da jam’iyyar PDP

- Ya kuma bayyana cewa APC na so zabe ya gudana a fadin Najeriya a rana guda

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu ya bukaci INEC da ta sauya wasu daga cikin manyan jami’anta.

Oshiomhole ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki na APC da ya gudana a Abuja.

Da dumi-dumi: Oshiomhole na so ayi sauyi a INEC

Da dumi-dumi: Oshiomhole na so ayi sauyi a INEC
Source: Depositphotos

Taron ya samu halartan shugaban kasa Muihammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, gwamnonin APC 11 da sauran shugabannin jam’iyyar.

Mista Oshiomhole ya zargi wasu kwamishinonin INEC da aiki tare da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Musamman ya ambaci sunan kwamishinan zabe a Akwa Ibom, Mike Igini, wani dan raijin kare jama’a a Najeriya.

Oshiomhole ya alakanta bukatarsa na cewa INEC ta sauya jami’anta da tawagar kwallon kafa da ke koragfi game da alkalin wasa mai son kai. Yace jami’an wasan na da hakkin sauya wannan alkalin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’an hukumar INEC za su sake zama

Mista Oshiomhole ya kuma zargi INEC da fallasa shirinta na dage zaben shugaban kasa a makon da ya gabata ga PDP.

Ya kuma bayyana cewa APC na so zabe ya gudana a fadin Najeriya a rana guda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel