Najeriya ta dukurkushe gabanin zuwan Buhari - Boss Mustapha

Najeriya ta dukurkushe gabanin zuwan Buhari - Boss Mustapha

Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha, ya yi karin haske dangane da turba da kuma tafarki na rashin aminci da Najeriya ke kai gabanin hawan shugaban kasa Muhammadu Buhari kujerar mulki a shekarar 2015 da ta gabata.

Babban sakataren gwamnatin kasar nan ya ce, Najeriya ta kasance akan mafi munin tafarki na rashin aminci da rashin nagarta gabanin hawan shugaban kasa Buhari da a yanzu ya ke ci gaba da dawo da martabar ta da kai wa zuwa tudun tsira.

Boss Mustapha tare da shugaban kasa Buhari

Boss Mustapha tare da shugaban kasa Buhari
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mista Mustapha ya yi furucin hakan a taron cibiyar tsare-tsare da ci gaban kasa, National Policy and Development, da aka gudanar a babban birnin kasar nan na tarayya.

Mista Mustapha wanda sakataren dindindin Olusegun Adeleke ya wakilta yayin babban taron, ya ce aminci gami da nagarta ke ayyana yanayi na gwamnatin shugaban kasa Buhari da a yanzu kasar nan ke ci gaba da moriyar hakan.

Ministan Abuja, Muhammadu Bello wanda ya wakilci shugaban kasa Buhari yayin taron ya bayyana cewa, kwazo gami da nasarorin gwamnatin sa tabbaci ne da ke nuni da cewa Najeriya za ta taka mataki na aminci tare da kai wa zuwa tudun tsira yayin jagorancin sa a karo na biyu.

KARANTA KUMA: Ka hakura da siyasa idan ka sha kasa a zaben 2019 - Matasan 'kabilar Ibo sun shawarci Buhari

Tsohon gwamnan jihar Borno da Legas a lokacin mulkin soja, Birgediya Janar Muhammad Buba Marwa, ya yi halartar taron ya yabawa kwazon gwamnatin shugaba Buhari musamman a bangaren assassa asusun gwamnatin na bai daya da a yanzu ta ke tanadin kimanin Naira miliyan 42 a kowane wata.

Janar Marwa ya ce shugaban kasa Buhari ya ci gajiyar Najeriya a yayin da ta ke mafi munin hali na durkushewa cikin dukkan bangorori da ya wassafa ka ma daga zangwayewar tattalin arziki, rashin ingatattun gine-gine, da ya ce a yanzu amince ya sauka a gare su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel