Yanzu Yanzu: Kotun Kano ta bayar da belin Deji Adeyanju

Yanzu Yanzu: Kotun Kano ta bayar da belin Deji Adeyanju

Wata kotun Majistare da ke jihar Kano ta bayar da belin Mista Deji Adeyanju, jagoran kungiya mai rajin kare hakkin yan Najeriya.

An tsare Adeyanju a wani gidan yari na Kano bayan rundunar yan sanda ta sake kama shi sannan ta tuhume shi da kisan kai.

An bayar da belin shi akan N50,000 da kuma wadanda za su tsaya masa mutum biyu, yayinda kotu ta kuma umurce shi da ajiye fasfot dinsa na fita waje.

KU KARANTA KUMA: An samu rabuwar kai a APC reshen Benue kan kudaden kamfen din shugaban kasa

Da yake tabbatar da belin da aka ba Adeyanju, Oluyemi Fasipe, daya daga cikin hadimansa yace: “Ina iya tabbatar maku da cewar an bashi beli. Belin ya hada da N50,000 da wadanda za su tsaya masa masu kadarori a Kano.”

Adeyanju ya shafe kawanaki 67 a gidan yari kafin a sake shi a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu.

A wani labari na daban, hukumar nan ta gyaran dabi'u watau Hisba ta jihar Kano dake a Arewa maso yammacin Najeriya tace ta soma tantance kimanin akalla maza da mata dubu takwas a cikin shirin nan nata na aurar da zawarawa da gwamnatin jahar ta shirya.

Tun a ranar 12 ga watan Disambar 2018 ne dai gwamnatin jahar ta kafa wani kwamitin mai mutun 23 domin tantance wadanda ake son aurarwa.

An dai ware aurar da 3000 daga cikin 8,000, bayan gano maza da mata 18 dauke da cutar HIV da kuma ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel