Yanzu-yanzu: Buhari, Osinbajo, gwamnonin APC sun dira taron gaggawa kan dage zaben INEC

Yanzu-yanzu: Buhari, Osinbajo, gwamnonin APC sun dira taron gaggawa kan dage zaben INEC

Shugaba Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) akalla 11 sun dira sakatariyar jam'iyyar dake birnin tarayya Abuja domin halartan taron gaggawa kan dage zabe.

A ganawar wand ake kan yi yanzu, shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, ya nuna rashin amincewarsu da jami'an hukumar INEC kan abubuwan suka biyo bayan dage zaben ranan asabar da ya gabata.

Daga cikin manyan jigogin APC dake taron sune babban jigon jam'iyyar, Ahmed Bola Tinubu, sakataren APC, Mai Mala Buni, diraktan kamfen APC, Rotimi Amaechi, shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan.

Daga cikin gwamnonin akwai na jihar Zamfara, Abdulaziz Yari; gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu; gwamnan jihar Osun, Gboyega Isiaka; gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi; gwamnan jihar Borno, Kashim shettima; gwamnan jihar Bauchi, Mohammad Abubakar.

Sauran sune gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello; gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode; da gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa'i.

Bayan jawabin shugaba Buhari, an bukaci yan jarida su fita daga cikin dakin taron saboda yan jam'iyyar za suyi tattaunawan sirri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel